1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsari ya kashe daliban ketare 13 a Spain

Zainab Mohammed AbubakarMarch 20, 2016

Daliban musaya na kasashen ketare 13 ne suka rasa rayukansu kana wasu masu yawa suka jikkata a lokacin da motar Bus da suke tafiya a cikinta ta yi hatsari.

https://p.dw.com/p/1IGgK
Spanien Busverunglückt
Hoto: Picture alliance/AP Photo

Daliban da ke cikin tsarin nan na musayan dalibai tsakanin kasa da kasa a gundumar Catalonia da ke yankin arewa maso gabashin Spain, sun fito ne daga kasashe daban daban 16 da suka hadar da Britaniya da Netherlands da Ukraine da Switzerland da Finland da Norway and Sweden da Japan da kuma New Zealand.

Dukkan daliban da suka mutun 'yan mata ne, a cewar gwamnan gundumar Carles Puigdemont, duk da cewar ba'a fadi kasashen da suka fito ba...

" Ya ce ina mika gaisuwar ta'aziyya zuwa ga wadanda hatsarin ya ritsa da su. Ina aika wannan jaje ne zuwa ga iyalan wadanda ke cikin hatsarin. Kana da sakon gaisuwa zuwa ga wadanda suka samu raunuka, kuma ke samun jinya a cibiyoyinmu na kula da lafiya. A yanzu haka muna tattara dukkan bayanai domin sanin musabbabin wannan mummaunan hatsari"

Ministan cikin gida na Spain Jorge Fernandez Diaz wanda ya gaggauta zuwa wurin hatsarin, ya ce har yanzu ya kasa gane dalilin da yasa matukin motar ya kaucewa hanya.