1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin Jirgin ƙasa a Indiya

July 19, 2010

Mutane a kalla 60 suka mutu a Hatsarin layin dogo da ya auku a gabacin ƙasar Indiya

https://p.dw.com/p/OOef
Hoto: AP

Sama da mutane 50 suka rasa rayukansu a wani haɗarin layin dogo da ya auku a Gabacin ƙasar Indiya.

Wani jirgin ƙasar wanda yake kan hanyasa ta zuwa Calcuta hed kwatar Bengale, ya ci karo da wani jirgin  dake a tsaye a wata tashar ta Birbhum inda ya dake shi ta baya,

abinda ya yi sanadiyar cirewar taragon baki ɗaya wanda galibi jamaar da lamarin ya rutsa da su a ciki ,suke.

Da ya ke magana da manema labarai wani jam'in 'yan sanda na yanki  ya shaida cewa haryanzu suna kokarin cire gawarwaƙin jama'ar daga cikin tarkaccen jirgin, sanan ya ce ba mamaki na gaba addadin  mutane da suka mutu a hatsarin ya ƙaru.

Wannan dai shine hatsarin jirgin ƙasar na biyu  da aka samu a yankin na Bengale, bayan wanda ya faru watannin biyu da su wuce wanda a cikinsa mutane 150 suka mutu wanda kuma aka ɗaura alhaƙinsa akan yan tawaye na Maoist.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar