1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HAUHAWAR TSAMARI TSAKANIN TOGO DA JAMUS

YAHAYA AHMEDMay 3, 2005

Kwana uku bayan cinna wuta a cibiyar al’adun nan ta Goethe da ke babban birnin kasar Togo, wato Lomé, Jamus ta ba da sanarwar dakatad da duk wasu huldodi a fannin al’adu da kasar ta yammacin Afirka. A bangare daya kuma, ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer, ya yi shawarwari da babban sakataren Majalisar dinkin Duniya Kofi Annan a birnin New York, kan tashe-tashen hankullan da suka barke a kasar Togon bayan zaben shugaban kasar da aka yi a makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/BvcC
Cibiyar al'adu ta Goethe a birnin Lomé, ta kone murkus bayan an cinna mata wuta a daren ranar juma'ar da ta wuce.
Cibiyar al'adu ta Goethe a birnin Lomé, ta kone murkus bayan an cinna mata wuta a daren ranar juma'ar da ta wuce.Hoto: dpa

Tun kafin a yi zaßen shugaban kasar Togon ne dai, aka fara samun hauhawar tsamari a huldodin dangantaka tsakanin wannan kasar ta Afirka Ta Yamma da Jamus. Da farko dai, ministan harkokin cikin gidan kasar, Francois Boko, ya nemi mafaka ne a ofishin jakadancin Jamus da ke babbabn birnin, wato Lomé, bayan an sauke shi daga mukaminsa kafin a yi zaben. Kazalika kuma, kafin a yi zaben ne jami’an ma’aikatar harkokin wajen Jamus, suka gana da shugabannin jam’iyyun adawan kasar don tattauna batun kare hakkin dan Adam. Bisa dukkan alamu, duk wadannan ba su gamsad da gwamnatin Togon ba. Sabili da haka ne kuwa, manazarta al’amuran da ke kai suna kawowa a harkokin siyasar kasa da kasa ke ganin cewa, harin da aka kai a kan cibiyar al’adun Goethe a ran juma’ar da ta wuce a birnin na Lomé, ba wani abin mamaki ba ne. Wato matakin mai da martani ne, da wasu da ke da jibinta da soji da kuma jami’an tsaron kasar suka dauka don bayyana fusatarsu da matsayin da Jamus ta dauka, musamman wajen sukar hukumomin kasar da take hakkin dan Adam. A halin yanzu dai, saboda hauhawar tsamarin da ake samu a dangantaka tsakanin kasashen biyu, ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta yi kira ga `yan kasarta da su fice daga Togon, a wani matakin riga kafin da ta dauka, don hana aukuwar irin abin da ya faru ga Faransawa a birnin Abidjan a kasar Côte d’Ivoire, a lokacin da wani rikici ya barke tsakanin gwamnatin kasar da ta Faransa. Bisa rahotannin da muka samu, kusan Jamusawa dari uku ne suka bi kiran gwamnatinsu, tuni suka fice daga Togon.

Masharhanta dai na ganin cewa, magoya bayan gwamnatin kasar Togon tare da daurin gindin wasu jami’anta ne ke da hannu a wannan hauhawar tsamarin da aka samu. Da farko dai, mahukuntan kasar na nuna bacin ransu ne da matakin da Jamus da kuma Kungiyar EU suka dauka kan Togon, na dakatad da duk wani taimakon raya kasa da suke ba ta, saboda take hakkin dan Adam da suke yi tun lokacin tsohon shugaba Eyadema. Kungiyar Hadin Kan Turan ta fara daukan wannan matakin ne a shekarar 1993, yayin da jami’an tsaro suka bude wa masu zanga-zanga ta hannunka mai sanda wuta a birnin Lomé.

Tun mutuwar tsohon shugaban kasar, Eyadema ne, kusoshin sojin kasar, suka yunkuri mika ragamar mulki ga dansa Faure Gnassingbe. Amma saboda matsa musu lamba da Kungiyar Tarayyar Afirka da gamayyar kasa da kasa suka yi ne, suka amince da shirya zabe. Sai dai ga shi kuma, ana zarginsu da tabka magudi a zaben. Faransa dai ba ta ce uffan ba game da zaben. A daura da zargin da ake yi kuma, Kungiyar Tattalin Afirka Ta Yamma, wato ECOWAS, ta ce an gudanad da zaben ne kamar yadda ya kamata ba tare da samun alamun wani magudi ba. Wasu masu sa ido daga kasashen Yamma dai sun ce, sun ga yadda aka yi ta fita da akwatunan zabe daga wasu rumfuna a ranar zaben, aka je aka kona su. Mutane da yawa da suka je ka da kuri’unsu kuma, ba su ga sunayensu a rajistar masu zaben ba. Sabili da haka, ba a yarda sun ka da kuri’un ba.

Masu sukar lamiri dai na zargin gamayyar kasa da kasa da yin zaman oho ba ruwanmu ne game da ababan da ke wakana a nahiyar Africa, har sai aski ya kai gaban goshi. Da tuni ta tsoma baki, da al’amura ba su tabarbare kamar yadda aka samu yanzu ba.

Babu shakka, Togon ba wata kasa ce mai arziki ko kuma albarkatun kasa ba. Sabili da haka, kasashen Yamma ma ba sa nuna sha’awa gare ta. Amma irin wannan rashin nuna sha’awar ne kuwa, ke janyo munanan halayen da ake samu a yankuna daban-daban na nahiyar Afirkan. Ganawar da ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer, ya yi da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a birnin New York a ran litinin da ta wuce, wani kyakyawan mataki ne wajen sassauta hauhawar tsamari a kasar ta Togo. Sai dai, da ya kamata a dau irin wannan matakin tun da wuri, ba sai an shiga cikin halin ni `yasu ba tukuna.

Kazalika kuma, sai gamayyar kasa da kasa tare da hadin gwiwar Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, wato ECOWAS, sun dau matakan yin katsalandan a Togon ne, za a iya kau da barkewar yakin basasa a kasar.