1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hayaƙi ya haifar da rufe filayen giragen sama a nahiyar Turai.

April 16, 2010

Tsaikon zurga zurgar jiragen sama a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/MyYJ
Hayaƙi ya mamaye sararin samaniya a nahiyar TuraiHoto: AP

Tokar hayaƙi da ta turniƙe sararin samaniya sakamakon aman wuta daga wani dutse a ƙasar Iceland ta haifar da soke tashi da saukar dubban jiragen sama a faɗin nahiyar Turai. Dubban ɗaruruwan Fasinjoji sun yi carko-carko a filayen jiragen sama yayin da ya zamewa hukumomi wajibi su dakatar da tashin jiragen. A nan Jamus an rufe filin jiragen sama na Frankfurt wanda ke zama na biyu mafi girman hada-hada a nahiyar turai. Jiragen da suka riga suka taso domin sauka a filin jirgin ana karkata akalarsu zuwa filin saukar jirage na Munich a kudancin ƙasar. Suma ƙasashen Birtaniya da Netherland da kuma Belgium sun rufe filayensu na saukar jirage. Tun a ranar Alhamis ne dai aka rufe filayen jiragen saman dake kudancin Jamus. Ana kyautata tsammanin hayaƙin tokar da ke yaɗuwa a gabashi da kudu maso gabashin nahiyar turai ka iya cigaba da shafar zurga zurgar jirage har nan da yan kwanaki masu zuwa. 

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala 

 Edita :        Umaru Aliyu