Hayatou ya sha kaye a zaben Hukumar CAF
March 16, 2017Talla
Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta zabi Ahmad Ahmad dan Madagaska a wannan rana ta Alhamis inda zai maye gurbin Issa Hayatou da ya dauki lokaci mai tsawo ya na jan ragama ta Hukumar CAF, abin da ke zuwa bayan zabe a taron kungiyar a kasar Habasha.Ahmad dan shekaru 57 da ke zama tsohon ministan gwamnati wanda kuma ke amfani da suna guda daya tilo ya samu nasara da kuri'u 34 da 20 a zaben shugaban na Hukumar CAF abin da ya kawo karshen shugabanci na shekaru 29 da Hayatou dan asalin kasar Kamaru ya kwashe ya na jan ragama ta mulkin wannan hukuma.