1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hidimomin girke dakarun UN a Lebanon.

Yahaya AhmedAugust 28, 2006

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya isa a birnin Beirut don tattaunawa da mahukuntan ƙasar Lebanon a kan batun girke dakarun kare zaman lafiya a yankunan kudancin ƙasar da ke iyaka da Isra'ila da kuma Siriya.

https://p.dw.com/p/BtyU
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi AnnanHoto: AP

Kawo yanzu dai, alƙaluman da aka tara game da yawan dakarun zaman lafiyar da Majalisar Ɗinkin Duniya da za ta girke a ƙasar Lebanon na nuna alamun cewa za a cim ma wannan burin. Tuni ƙasar Italiya ta ce za ta ba da gudmmowar dakaru dubu 3, Faransa dubu 2, Finnland kuma ɗari 2 da 50. Masu tsara shirye-shiryen ayyukan kare zaman lafiyar a birnin New York dai na kyautata zaton cewa, za a iya girke dakarun cikin lokaci. Amma duk da haka, da akwai wasu matsaloli da ba a warware su ba tukuna. Cornelia Franke na ɗaya daga cikin masu tsara shirye-shiryen na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

„Bisa dukkan alamu, muna samun goyon baya daga wasu ƙasashen Turai. Amma kamata ya yi mu ƙara samun gudummowa daga wasu yankunan kuma, kamar na Asiya alal misali.”

Wato jami’an Majalisar dai na ganin cewa, bai dace a girke dakarun Turai kawai a kudancin Lebanon ɗin ba. Ƙasashen musulmi na Asiya ma na da tasu gudummowar da ya kamata su bayar. Amma matsalar da ta kunno kai a nan, ita ce, Isra’ila, har ila yau ta ƙi amincewa da girke dakaru daga ƙasashen Malaysia, da Indonesia da kuma Bangladesh. Gwamnatin ƙasar bani Yahudun ta ce ba za ta amince da girke dakarun duk wata ƙasar da ba ta da hulɗa da ita a kan iyakarta ba. Za ta fi gwammacewa ne da dakaru daga Masar da Jordan da kuma Turkiyya. Amma Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta sami alakawarin waɗannan ƙasashen ba, na ba da gudummowar soji.

Abin da ake da tabbaci a kansa a yanzu, shi ne, bisa yarjejeniyar da aka cim ma a birnin Brussels a ranar juma’ar da ta wuce, za a iya tura farkon tawagar da ta ƙunshi dakaru dubu 3 da ɗari 5 zuwa kudancin Lebanon ɗin a cikin lokaci. Ana kyautata zaton cewa, a ran laraba mai zuwa ne rukunin farko daga kasar Italiya zai isa a Lebanon ɗin. Ba za a dai ɓata wani lokaci na dogon turanci ba. Ko yaushe dakarun wata ƙasa suka shirya, za su tashi kai tsaye zuwa yankin.

A wannan karon dai, za a bai wa dakarun kare zaman lafiyar cikakken iko ne fiye da rukunin sa ido da majalisar ta girke a da a yankin. Za su iya kai farmaki ga masu take ƙa’idojin yarjejeniyar da aka cim ma, idan rundunar sojin Lebanon ɗin ta bukace su su yi haka don mara mata baya. Siriya dai ta nuna adawarta ga wannan matakin, saboda a kan iyakarta da Lebanon ɗin mai tsawon kilomita ɗari 3 da 75 ma, rundunar kare zaman lafiyar za ta iya aiwatad da wannan umarnin.

A yau ne dai jami’an Majalisar Ɗinkin Duniyar za su yanke shawara kan yadda za a rarraba dakarun da kuma inda za a girke su. An dai sami ƙasashe da dama da ke ba da gudummowar dakarun rundunar mayaƙan ruwa, a cikinsu kuwa har da Jamus. Game da yadda za a rarraba dakarun dai, Conelia Franke ta bayyana cewa:-

„Ita Majalisar Ɗinkin Duniyar ce za ta yanke shawara kan yadda rundunar za ta kasance. Kuma tana hakan ne tare da tuntuɓar hafsoshin kula da tsarin dakarun. Sai dai a ƙarshe, malajalisar kaɗai ce ke da ikon yanke shawara.“

Kafin zuwa watan nuwamba dai ana zaton cewa za a iya girke dakaru dubu 12 a yankin na kudancin Lebanon. Ban da dakaru dubu 2 na rukunin sa ido da tuni yake can, ana bukatar rukunin farko ne da ya ƙunshi dakaru dubu 3 da ɗari 5. Daga bisani kuma za a sake tura wani rukunin mai yawan dakaru kamar na farkon. Sa’annan daga baya kuma, a ƙara tura wata tawagar mai dakaru dubu 3.