1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillari Clinton ta bayyana shawar tsaya takara shugaban ƙasa

January 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuTu

Matar tsofan shugaban ƙasar Amurika, Bill Clinton, ta bayyana shawar ta, ta shiga takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurika, na watan november shekara ta 2008.

Hillary Clinton,ta bayyana wannan aniya, ranar jiya assabar, inda kuma ta bukaci Amurikawa, su bata shawarwari, a game da wannan yauni da ta ke shirin runguma:“

„A yau, ina farin cikin bayyana cewar, na girka komitin da zai tunani, a kan takara ta, ta neman muƙamin shugaban ƙasar Amurika.

Saidai hakan, bai nufi, da na fara yaƙin neman zaɓe.

Amma inna buƙatar shawarwari daga Amurikawa, domin lokaci yayi, inda ta kamata baki ɗayan mu, mu yi tunani a kan hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin Iraki, da farfaɗo da martabar Amurika a idan dunia.

Kazalika, mu yi tunani a kan yadda za mu sami yanci, ta fannin makamashi, paƙat!!!, mu sami sabin hanyoyin kyauttata makomar Amurika da Amurikawa“.

Idan Jam´iyar Demokrate ta tsaida Hillari Clinton yar takara, ta kuma samun nasara lashe zaɓen, zata kasance macce ta farko, da ta za hau matsayin shugaban ƙasa a Amurika.