1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton: matsalar mallakar wasikun sirrin kasa

Gazali Abdou TasawaSeptember 1, 2015

Wata kotun Amirka ta bada umarnin adana wasu wasikun sirri da ake zargin Hillary Clinton da mallaka a lokacin tana rike da mukamin ministan harakokin wajen kasar.

https://p.dw.com/p/1GOpu
Hillary Clinton
Hoto: Reuters/B. McDermid

Wata kotun kasar Amirka ta bada umarnin sake adana wasu wasiku kimanin 100 na tsohuwar sakatariyar harakokin wajen kasar Hillary Clinton daga cikin wasu jerin wasikun sama da 400 da aka bayyana wa jama'ar kasar a yammacin jiya Litanin. Kotun ta bukaci a yi hakan ne a bisa hujjar cewa wasikun na kunshe ga alamu da wasu batutuwa na sirri.

Yau makonni da dama kenan dai, wannan batu na wasu sakonnin sirri na kasa da ake zargin tsohuwar sakatariyar harakokin wajen kasar ta Amirka da boyewa ke dagula mata harakokin yakin neman zaben da ta ke yi na neman tsayawa takara a zaben shugaban kasar ta Amirka na shekara ta 2016.

Kotun kasar ta Amirka dai na Zargin Hillary Clinton da karba ko aika wasu sakonnin sirrin kasa har dubu 62 da 320 ba ta hanyoyin da dokar kasar ta tanada ba.