1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hira da shugaban Najeriya kan harkokin tsaro

Ubale MusaOctober 30, 2015

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan yakin da sojojin kasar ke yi da Boko Haram, inda ya nanata cewa za su kawo karshen yaki na gaba da gaba a zuwa karshen shekara.

https://p.dw.com/p/1GxF6
Muhammadu Buhari
Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

Hira da shugaban Najeriya kan harkokin tsaro

A kwanakin nan sojoji na korafin rashin kyawon yanayi da kuma batun kayan aiki a matsayin barazana, wannan zai shafi wa'adin da ka bayar na kawo karshen wannan yaki zuwa karshen shekara?

Wadanda suka san halin da ake ciki a lokacin da wannan gwamnatin ta zo, da halin da ake cikin yanzu an san akwai banbanci, tunda manyan hafsoshi duk an cire su kuma an canza su da wasu kuma aka canza musu wurin aiki, sannan su kansu sojojin aka kara horas da su, aka kara musu kayan aiki kuma ana cikin kara musu kayan aiki kuma suna cin nasara akan wannan yaki da ake yi. Su mutanen Yobe, da mutanen Borno da Adamawa, da Gombe yawanci inda su 'yan Boko Haram suka fi aikata ayyukan ta'addancin na su sun san akwai banbanci.

To amma kuma ba dole ba ne a kawo karshen wannan yaki zuwa karshen watan Disamba?

Aa shi yaki kamar yadda muka ce yaki na gaba da gaba za'a iya gamawa, amma ta'addanci da suke yi na kai hare-hare a Masallatai ko a Majama'u, ko a kasuwa, ko a tashar mota, ko yara suna bacci a makarantu su yanka su, to kaga wannan ba addinin Muslunci ba ne, ba addinin da ya yadda a ci mutuncin wani bare ma har a nakasa shi. Wanda ya yadda da Allah bayya cuta.

Hira da shugaban Najeriya kan harkokin tsaro

A wannan mako sojoji sun fitar da sunayan wasu mutane a kalla 100 'yan kungiyar ta Boko Haram, inda suka ce suna neman su ruwa a jallo, wannan yana nufin kun fidda fatan tattaunawa da su kenan?

Aa ai masu karin magana ke cewa ana bikin duniya ake na kiyama, tunda sun fito ana fada da su, ana karkashe su, idan har akwai manyan su wadanda suka ce za su yi magana su hana su, ko kuma su maido mana da 'yan matan nan da suka dauka na Chibock ai sai a yi magana da su.

To mu tabo batun yaki da cin hanci wanda shima kake cikinsa a yanzu, ko ka gamsu da yadda wannan yakin ke tafiya?

Ee wannan lokaci ne mai wahala, domin idan 'yan Najeriya za su iya tunawa a lokacin mulkin soja, ai kaga wadanda ake zaton sun ci hanci da rashawa din, tattarasu aka yi aka ajiye su, sannan aka kai su gaban shari'a. To yanzu ana cikin demokaradiyya, domokaradiyya kuma kowa ji yake yi komai ya yi idan ba an kama shi ba, da shi da mai kamanta gaskiya duk daya suke. Sabo da haka yanzu dole sai mun samu takardun wadanda suka yi barna sannan a kai su gaban kotu kuma wannan ba karamin aiki ne ba saboda tsananin cin hanci da rashawa da ya shiga cikin al'amarin Najeriya.