1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hira da Youssouf N´Dour

Harjes, Christine / DWApril 18, 2008

Youssouf N´Dour ya shahara wajen fitar da waƙoƙin Afirka a duniya

https://p.dw.com/p/DkDz
Youssou N' dour a fagen wasa na birnin KolonHoto: DW/Harjes, Ogunsade

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

To shirin na mu na yau zai yada zango ne a birnin Kolon na nan Jamus inda kwanakin baya mashahurin mawaƙin nan na ƙasar Senegal Youssou N´Dour ya jagoranci wani ƙasaitaccen buki waƙoƙi. Bayan wannan wasa DW ta samu zantawa da N´Dour inda ya yi bayani game da salon waƙarsa da tasirin waƙar musamman a nahiyar Afirka da kuma fatan sa ga wannan nahiya wadda ƙasashen yamma ake ma ta kallon wata matalauciyar nahiya mai fama da rikice rikice da wahalhalu iri daban daban.

A cikin shekaru 30 da suka wuce ba bu wani mahaluƙi da ya fito da waƙoƙin nahiyar Afirka ya alla a cikin nahiyar ko a wajen ta kamar Yousof N´Dour. Babu ɗaya daga cikin mawaƙan wannan nahiya da ya yi harhaɗa waƙoƙi na haɗin guiwa da shararrun mawaƙa da makiɗa na duniya da ya kai wannan mawaƙi ɗan ƙasar Senegal. Ya taka rawar gani wajen ƙarawa fannin kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe na nahiyar Afirka armashi sakamakon sabon salonsa na harhaɗa waƙoƙi. Wani aikin haɗin guiwa da suka yi da Peter Gabriel da Sting da kuma waƙar da suka yi da Neneh Cherry mai taken Seven Seconds a shekara 1994 ta ƙarfafa matsayinsa a jerin sanannun mawaƙa na duniya baki ɗaya. Sau uku da shi da Dido suna jagorantar bukukuwan waƙa na Live 8 da aka gudanar a biranen London, Paris da kuma Cornwell a shekara ta 2005.

Yousouf N´Dour wanda ya taɓa samun lambar yabo mafi girma da ake bawa shahararrun mawaƙa wato Grammy, shi ne jakadan asusun taimakon yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF. Sunansa kaɗai ya na matsayin wata alama ta sanannun waƙoƙi a duniya baki ɗaya. Tun shekaru da dama da suka wuce Yousouf N´Dour ke taka rawar ganin a fagen wakoƙin zamani a ƙasar wato Senegal. Yanzu haka dai ana saka shi a jerin mawaƙan nahiyar Afirka ƙalilan da suka yi fice wajen haɗa waƙoƙi masu daɗin ji da nishaɗantarwa a duniya baki ɗaya. Jaridar New York Times a kasar Amirka ta taɓa bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka fi iya waƙa a duniya sannan mujallar Time kuma ta sanya sunan sa a jerin mashahuran mutane 100 waɗanda suka canza zamantakewa a duniya.

Duban dubatan mutane masu sha´awar waƙoƙinsa suka hallara a zauren cashewa na Tanzbrunnen dake birnin Kolon lokacin da Yousouf N´Dour ya yi wasa. Hatta mawaƙa a duniya baki ɗaya suna sha´awar waƙoƙin wannan taliki daga Senegal. Ko shin ina ya samo wannan hazaƙa da basira ta haɗa waƙoƙi? Ta wata hanya yake samun ƙwarin guiwa yin waɗannan waƙoƙin? Yousouf N´Dour ya yi bayani yana mai cewa.

"Na fi samun kwarin guiwa daga ƙasa ta ta asali wato Senegal, inda na ke da zama kuma ina tafiyar da rayuwata ta yau da kullum. Dukkan abubuwan da na ke gani a zahiri musamman na rayuwa a ko-wace ranar Allah Ta´ala suna ƙarfafa mini guiwa a cikin wannan sana´a ta waƙa. Wasu abubuwan da suke burge Yousouf N´Dour sun haɗa yanayi da kuma al´umar ƙasarsa. "

A matsayinsa na ɗan Adam akwai wasu abubuwa da yake sha´awa akwai kuma waɗanda ya tsana. To amma a taƙaice dukkan waɗannan abubuwa suna ƙarfafa masa guiwa a waƙoƙinsa. A saboda haka duk fitan da yayi zuwa ƙetare ya kan tattara ra´ayoyi masu nasaba da ƙasarsa. Ba kamar wasu shahararrun mawaƙan Afirka ba waɗanda ke ƙaura daga ƙasashensu zuwa ƙasashen ƙetare don ci-gaba da rayuwarsu a can, shi dai N´Dour har yanzu a ƙasar sa wato Senegal ya ke. Ko shin menene dalilin haka?

"Abin da ya sa ban yi ƙaura ba. Ai abu ne mai sauƙi. Domin na fin jin daɗin zama a Senegal. Da farko dai ba ni da wata matsala idan ina son barin ƙasar. Akwai filin jirgin sama inda daga can ina iya tashi zuwa ƙetare cikin sauƙi ba da wata tsangwama ba. To amma a gaskiya na samun walwala a cikin ƙasa ta. Kuma hakan ya fi."

A wannan marra da muke ciki ´yan Senegal musamman matasa suna bi ta hanyoyi masu haɗari don tserewa matsalolin rayuwa ta yau da kullum a Senegal. Mafi yawa daga cikin su na ƙoƙarin shigowa nahiyar Turai ne. A kan haka N´Dour ya shirya wata waƙa mai taken Tukki, inda ya a cikin ya yi bayani dangane da tafiya zuwa Turai.

"´Yan Senegal sun yi suna wajen tafiye tafiye zuwa ƙetare. Ko shakka babu ana fama da matsalolin tattalin arziki a ko ina cikin duniya. Hakan ya sa mutane ba sa samun isassun guraben aikin yi kana kuma ba su da wata kafa ta ficewa daga  wannan matsala. Hotunan da suke gani a akwatunan telebijin daga Turai yana ruɗinsu cewa rayuwa na da sauƙi a wannan nahiya. Saboda haka suke ɗaukar wannan kasada. Bai dace ba yadda suke saka rayukansu cikin haɗari. Yana da kuma muhimmanci al´uma su samu walwala a cikin ƙasa."

N´Dour yayi imani cewa waƙoƙinsa suna da tasiri a rayuwar al´umar Senegal. Domin waƙa ka iya sa mutum yin zurfin tunani. Hakazalika N´Dour yana waƙa game da makomar Afirka. A ma wasan da yayi a Kolon ya bayyana cewa a Turai ba a ba da labarai masu daɗin ji game da Afirka. Ko shin ta ina ya ke ganin Afirka zata samu kyakkyawar makoma? Daga ina za a samu canjin da Afirka ke buƙata?

"Daga matasan Afirka waɗanda suka naƙalci kabli da ba´adi na inda duniya ta dosa, waɗanda kuma suke ƙaunar wannan nahiya a zucci. Na yi imani cewa waɗannan mutanen za su iya canza makomar Afirka. Afirka dai ba matalauciyar nahiya ba ce kamar yadda ake faɗi. Nahiya ce mai albarkatu iri daban daban. Saboda haka idan aka samu shugabanni adalai wannan nahiya za ta fita daga cikin ƙangin wahalhalu da take ciki."

A ƙarshe Youssouf N´Dour yayi fatan cewa nan ba da daɗewa ba za a samu haɗaɗɗiyar nahiyar Afirka inda za´a samun zaman lafiya, ´yancin faɗin albarkacin baki da kuma bawa kowa ´yanci daidai wa daida.