1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hirar da tashar Deutsche Welle ta yi da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer.

Mohammad Nasiru AwalMarch 26, 2004
https://p.dw.com/p/Bvl1
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka FischerHoto: AP

Tuni dai aka fatattaki gwamnatin kungiyar Taliban, amma duk da haka babu wani labari mai dadin ji da ake samu daga Afghanistan. A yankuna da dama na wannan kasa ana ci-gaba da dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin da basa ga maciji da juna, sannan harkokin tsaro sun tabarbare yayin da gwamnatin tsakiya kuma ba ta da angizo a wasu sassa na kasar. Hatta shirin da ake yi da nufin tada komadar tattalin arziki da sake gina wannan kasa ya na tangan-tangan. Yayin da fataucin miyagun kwayoyin kuma ke dada habaka, inda yanzu Afghanistan ke sahun gaba a jerin kasashen duniya da suka fi noman ganye opium da ake harhada hodar ibilis da shi. A takaice dai babu wani labari mai karfafa guiwa daga wannan kasa, to amma ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yayi nuni da cewa an samu canje-canje masu fa´ida a Afghanistan, sakamakon kasancewar kasashen duniya a kasar.

"Idan muka waiwayi baya zamu ga cewar an cimma wasu abubuwa masu yawa. Idan muka hango gaba zamu ga cewar da sauran rina a kaba. Da akwai yankunan da aka samu nasarar maido da da zaman lafiya da tsaro, kuma mutane na tafiyar da rayuwarsu kamar yadda aka saba. Haka zalika miliyoyin ´yan gudun hijira sun koma gida. A lokaci daya kuma ana fama da rashin kwanciyar hankali a yankunan kudanci da gabashin kasar. An yi nasarar dinke barakar dake tsakanin da yawa daga cikin kungiyoyin da ke gaba da juna, sannan kafa majalisar Loya Jirga wata babbar nasara ce. Sannan ana kara samun ci-gaba a aikin sake gina kasar. To sai dai idan muka dubi matsalar fataucin miyagun kwayoyi to sai in ce da sauran aiki a gaba."

Kasar dai ta fi fuskantar matsalar rashin kudi. Duk da alkawarin da aka yi na baiwa Afghanistan taimakon kudi dala miliyan dubu 4.5 a gun taron kasashen duniya da ya gudana a birnin Tokyo a shekara ta 2003, har yanzu kasar ba ta ga wani abin da ya taka kara ya karya ba.

Amma Jamus kamar yadda Joschka Fischer ya nunar, ta cika alkawuran da ta dauka, sannan ya ce zai yi duk iya kokarin ganin sauran kasashen duniya sun bi sahun Jamus a gun taron da za´a yi a birnin Berlin daga ranar 31 ga watan maris zuwa daya ga watan afrilu.

"Babbar manufar mu kuma abu mai muhimmanci, shine dukkan mu, mu san cewa dole ne mu cika alkawuran da muka dauka tare da kara ba da himma. Ba zamu nuna gajiyawa ba, har sai dukkan kasashen dake tallafawa wannan kasa sun sauke nauyin dake wuyansu. Aikin sake gina wannan kasa a fannoni da dama kamar farfado da tattalin arzikinta, gina makarantu da samar da tsarin kiwon lafiya mai nagarta zai taimaka ba kawai ga Afghanistan ba, a´a har da yakin da ake yi da ´yan ta´adda na kasa da kasa."

Ministan harkokin wajen na Jamus ya ce kasar Afghanistan na kan gaba a manufofin gwamnatinsa game da kasashen ketare. Kuma Jamus zata ci-gaba da taka muhimmiyar rawa a kokarin da ake yi na samarwa al´umomin Afghanistan wata makoma ta gari.