1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Holland: Jam'iyyar Firaminista Mark Rutte ta yi nasara

March 16, 2017

Kasashen duniya na ci gaba da taya firaministan kasar Holland Mark Rutte murnar nasarar da jam'iyyarsa ta samu a zaben kasar da aka yi na ranar Laraba.

https://p.dw.com/p/2ZISc
Niederlande Wahlen Mark Rutte in Den Haag
Firaministan kasar Holland Mark RutteHoto: picture-alliance/dpa/D. Reinhardt

Bangaran firaminista Mark Rutte na kasar ta Holland, ya sami akasarin kuri'u ne a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar fiye da babban abokin hamayyarsa Geert Wilders dan jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya da ke kyamar Musulunci da Musulmai, da kuma yake adawa da Kungiyar Tarayyar Turai. Da farko dai binciken jin ra'ayin jama'a ya nunar cewa Mista Wilders zai iya cin nasara a wannan zabe amma kuma sai bangaran na shi ya kare da kujeru 20 kacal, yayin da Firamiminista Rutte ya samu 33. Dan jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya Geert Wilders ya yi wa manema labarai bayani kan sakamakon da aka samu.

Zamu ci gaba da aiki don samun nasara a gaba

Deutschland Geert Wilders in Koblenz
Babban dan adawa na kasar Holland Geert WildersHoto: picture-alliance/dpa/T. Frey

"Na yi niyyar gwagwarmaya matuka. Zan ce muna cikin wadanda suka yi nasara a wannan zabe, sai dai abin takaici ba mu ne muka sami rinjayen kuri'u ba. Dole mu jira zabe na gaba. Sai dai jam'iyya ta bata fadi ba, don mun ci wani rukuni na kujeru, kuma ina alfahari da hakan."

Shi ma dai firaminista Mark Rutte cikin farin ciki ya nuna gamsuwarsa da wannan sakamako, inda ya jinjinawa magoya bayansa da jam'iyyarsa kan wannan nasara:

Firaminista Rutte ya samu kwarin gwiwa

Niederlande Anhänger von Mark Rutte in Den Haag
Magoya bayan Rutte na nuna murnarsu ta cin zabeHoto: picture-alliance/AP Photo/P. Post

"Wannan nasara ce ta jam'iyyarmu, ni ne kuma shugabanta a yanzu, gamayyar mai dubban al'umma daga sassa daba-daban da suka hada karfi don raya jam'iyya. Ina matukar alfaharin cewa mu ne babbar jam'iyya karo na uku."

A zaben na ranar Laraba dai, jam'iyyun Christian Democrat da Progress D66, sun samu kujeru goma 19 ne kowannensu, yayin da jam'iyyar ma'aikata mai kawance da gwamnati ta sha mumunar kaye da kuri'u tara (09), akasin 38 da ta ke da su a baya. Jamiyyar masu kare muhalli kuwa, ta tashi ne da kujeru 16 a zaben. Firaminista Mark Rutte, ya samu kujeru wakilan majalisa 33 ne cikin 150 da ake da su a kasar, kasa da kujeru 41 da jam'iyyar ta samu a shekara ta 2012.