1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

151008 Ausbildung Migranten

Ripperger, Sabine (DW Berlin) November 5, 2008

Wata ƙungiyar Turkawa ´yan kasuwa da masu sana´o´in hannu a Berlin wato TUH a taƙaice ta duƙufa wajen samarwa baƙi matasa guraben koyon sana´o´i a faɗin nan Jamus.

https://p.dw.com/p/Fo1r
´Yan matan Turkawa ´yan makaranta a JamusHoto: picture-alliance/ dpa

Wata ƙungiyar Turkawa ´yan kasuwa da masu sana´o´in hannu a Berlin wato TUH a taƙaice ta duƙufa wajen samarwa baƙi matasa guraben koyon sana´o´i a faɗin nan Jamus. Ƙungiyar wadda aka kafa ta a cikin shekarar 2005, ta fara ne bisa manufar taimakawa kamfanoni mallakar ´yan asalin Turkiya a birnin Berlin. To sai dai ta faɗaɗa ayyukanta inda yanzu take kula da wasu ɓangarori, ciki har da ƙaddamar da wasu aikace-aikace ga yaran da suka katse karatun boko, cibiyoyin ba da shawarwari musamman waɗanda suka shafi yanayin zama cikin ƙasar da batutuwa na shari´a sai kuma wuraren taruka tsakanin iyaye mata. Wata nasarar da ta samu a baya-bayan nan shi ne kammala wani kwas na watanni huɗu inda aka horas da matasa musamman ´yan asali da ƙasar Turkiya sanin makaman aikin jiya da kula da tsofaffi. To shirin mu kewaya Turai na lokacin zai duba ƙoƙarin da baƙi mazauna nan kasar ke yi ne na tsame kansu daga cikin matsalar rashin aikin yi.

Wannan ƙungiyar ta Turkawa ´yan kasuwa da masu sana´o´in hannu a Berlin wato TUH a taƙaice yanzu dai ta faɗaɗa ayyukanta daga mai kula da buƙatun ´yan kasuwa zuwa mai samarwa baƙi matasa guraben koyon sana´o´i a faɗin wannan ƙasa. Hüssein Yilmaz shugaban wannan ƙungiya ya bayyana dalilin da ya sa suka fara gabatar da kwasa-kwasai yana mai cewa.

“Muna da baƙi ´yan ci-rani da yawa a nan, waɗanda yanzu wasunsu sun tsufa. Da yawa daga cikinsu na buƙatar taimako. Amma idan aka yi amfani da harsunansu na asali wajen kula da waɗannan mutanen an fi samun biyan buƙata, domin ana ƙara samun yarda da juna. Saboda haka yanzu ana samun ƙaruwar masu neman taimako daga garemu.

Ganin yadda ake fama da yawan marasa aikin yi musamman tsakanin matasa ´ya´yan baƙi, ya sa aka yi tunani mai zurfi kan yadda za a bawa wannan rukunin na jama´a da ba su da cikakkiyar ƙwarewar aiki, wata damar samun aikin yi a fannonin kula da tsofaffi. Alal misali ana fama da ƙarancin ma´aikata musamman waɗanda suka iya harshen Turkawa da za su kula da tsofaffi ´yan asalin ƙasashen waje. A saboda haka sashen tattalin arziki da fasaha batutuwan da suka shafi mata na majalisar birnin Berlin yake tallafawa wannan shiri, kamar yadda sakatariyar ƙasa Almuth Nehring-Venus ta jaddada a baya-bayan nan.Ta ce a cikin shekaru kaɗan masu zuwa za a samun ƙarin guraben aiki a fannonin kiwon lafiya, jiya da kuma na shaƙatawa.

“Muhimmin abu a gare mu shi ne mu ga an samu ƙaruwar baƙi mazauna a wannan birni na Berlin kuma masu ƙwarewa a fannoni daban daban a kasuwar ƙwadago domin samu aikin yi. Bayan ziyarce-ziyarce da na kai a cibiyoyi da sauran wuraren kula da tsofaffi a nan Berlin na shaidar da cewa akwai guraben aiki da yawa. Alal misali Can Vital wadda ta ƙware wajen kula da tsofaffi da marasa lafiya ´yan asalin Turkiya, sun ce a wannan shekarar za su iya ɗaukar ma´aikatan jiya to amma bisa sharaɗin cewa sun iya harshen Turkawa.”

Da yawa daga cikin waɗanda suka sauke karatu sun cike wannan sharaɗi saboda haka suna da kyakkyawar damar a kasuwar ƙwadago. Su ma masu asali da ƙasashen Larabawa da suka yi kwas ɗin za su iya samun aikin yi a cibiyoyin kula da ´yan kasarsu. A cikin farin ciki da annashuwa shugaban ƙungiyar ta Turkawa ´yan kasuwa da masu kamfanoni Hüssein Yilmaz ya nuna sakamakon kwas ɗin da aka kammala kwanan nan.

“Mutane huɗu daga cikin waɗannan tara za su samu karɓuwa nan-take a kasuwar ƙwadago. Ko da yake muna fuskantar wasu matsaloli amma za mu yi nazari kansu domin mu yi gyara a cikin kwas na gaba.”

Da malamai takwas aka gudanar da wannan kwas tsawon watanni huɗu sa´o´i bakwai a kowace rana. Bayan kwas ɗin an tura su wani wurin jiya inda suka koyi aikin tsawon watanni uku. Daga cikin maza ƙalilan da suka halarci kwas ɗin shi ne Mahir, matashi dan asalin ƙasar Turkiya. Ko shin me ya koya a wajen kwas ɗin, Mahir sai ya kada baki ya ce.

“Gaskiya na koyi abubuwa da yawa wato kamar buƙatun yau da kullum na ɗan Adam. Yanzu dai mun san abin da ake nufi. Mun koyi irin taimakon da mutum ke buƙata da kuma irin taimakon da mu kanmu masu taimakawa za mu iya buƙata. Burinmu shi ne mu taimakawa mutane ´yan´uwanmu.”

Mahir yana tattare da kyakkyawan fatan cewa nan ba da jimawa zai samu aiki a wsata cibiyar kula da mutane masu asali da ƙasashen ƙetare.

“E ƙwarai ko shakka babu wannan shi ne ƙoƙarin da muke yi domin kawo ƙarshen rashin aikin yi musamman a tsakanin baƙi.”

Ita kuwa Hülya mai shaekaru 27 da haihuwa cewa ta yi ya zama wajibi mutum ya gudanar da wannan aiki tsakani da Allah.

“Dole ne ka nuna sha´awarka ga aikin da ka zaɓarwa kanka. Ta haka ne za a ji daɗin yin wannan aiki. Idan ba ka sha´awar aikin, ka ga ba za ka iya tsaya ka yi shi tsakani da Allah ba. Wani lokacin dai wannan aiki na mu ya dogara ga kamfani da kuma ma´amala tsakanin ma´aikatansa.”

Tun gabanin wannan kwas Zübeyde ´yar asalin Turkiya ta yi aiki a fannoni daban daban kama daga wurin sayar da nama ya zuwa wuraren wanki da guga. Amma daga baya ba ta rasa aikinta. Saboda haka take murnar ƙwarai da gaske game da wannan horaswa da ta samu a matsayin mataimakiyar mai yiwa mutane jiya. Zübeyde ta fi gamsuwa da wurin koyon aiki domin ta samu damar saduwa da mutane kai tsaye kana kuma ta koyi yadda ake hulɗa da tsofaffi. To sai dai yaya take hangen aikin da za ta samu nan gaba?

“Ina fata zan samu aiki mai kyau inda zan yi aiki lafiya lau da sauran mutane don taimakawa tsofaffi da sauran mabuƙata.”

A halin da ake ciki Zübeyda ta fara tattaunawa da wata cibiyar kula da tsofaffi ta ´yan Turkawa dake unguwar Wedding a Berlin, inda take fatan fara aiki nan ba da jimawa ba.