1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW ta soki kisan 'yan shi'a a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 23, 2015

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce kisan da sojoji suka yi wa Musulmi mabiya Shi'a a Zaria ta tarayyar Najeriya, sun yi ne ba tare da wani dalili ba.

https://p.dw.com/p/1HS2f
'Yan shi'a na fuskantar kisa daga sojoj a Najeriya
'Yan shi'a na fuskantar kisa daga sojoj a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

A wata sanarwa da ta fitar da sanyin safiyar Larabar nan, kungiyar ta ce sojojin sun fara bude wa yara 'yan shi'a wuta kafin ma wata takaddama ta hadasu, kana daga bisani suka kaddamar da farmaki da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mabiya shi'ar marasa rinjaye a yammacin Afirka, a garin Zaria da ke jihar Kaduna a Tarayyar Najeriya.

Wannan batu na Human Rights Watch na zuwa ne a dai-dai lokacin da majalisar Musulunci ta Najeriya ta gargadi gwamnati da kada ta sake janyo abin da zai haifar da wata kungiya bayan wadda ake fama da ita a yanzu ta Boko Haram wadda ta yi sanadiyyar mutuwar sama da 'yan Najeriya 20,000.

Kungiyar Human Rights Watch da ke da matsuguninta a birnin New York na Amirka ta bayyana cewa akallah mutane 1,000 ne mabiya shi'a suka rasa rayukansu yayin farmakin da sojojin Najeriya suka kai musu a ranakun 12 zuwa14 ga wannan wata na Disamba da muke ciki a garin Zaria da ke jihar Kaduna a Arewacin Najeriyar.