1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW ta zargi gwamnatin Sudan da aikata kissan kiyasu a yankin Darfur

September 7, 2006
https://p.dw.com/p/BukO

Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama, Human Rigth Watch, ta zargi hukumomin Sudan, da aikata kissan kiyasu ga al´ummomin yankin Darfur.

Kakakin hukumar, Peter Takirambude, ya ce binciken da su ka gudanar ya gano hanyoyin da dakarun gwamnati ke bi, domin hallaka al´ummomin da ba su ji, ba su gani ba, tare da anfani da bama bamai.

Sudan ta bayyana aniyar jibge, dakaru dubu 10 a wannan yanki, domin maye gurbin sojojin shiga tsakani na ƙungiyar taraya Afrika.

A wata sanarwa da ta hido jiya laraba, fadar gwamnatin Amurika, ta bukaci sojojin AU, su ci gaba da zama, a yankin, kamin ya´Allah Sudan, ta amince karɓar rundunar shiga tsakani ta MDD.