1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hugo Chavez na Venezuela ya sha kaye

Ibrahim SaniDecember 3, 2007
https://p.dw.com/p/CVvr

Shugaba Hugu Chavez na Venezuela ya sha kaye a game da shirinsa na yin garanbawul, a kundin tsarin mulkin ƙasar. Hakan ya biyo bayan sakamakon zaɓen raba gardama ne da aka gudanar a ƙasar. Kashi 51 cikin ɗari na ma su zaɓen ne su ka yi watsi da wannan shiri na shugaba Chavez. An dai gudanar da zaɓen ne bisa manufar gudanar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar. Batun wa´adi na shugaban ƙasa da kuma cikakken ikon shugaban babban bankin ƙasar na daga cikin abubuwan da gyaran zai shafa. Jam´iyyun adawa na ƙasar sun zargi shugaba Hugo Chavez da ƙokarin gudanar da gyare-gyaren, don yin tazarce a gadon mulkin ƙasar. To amma rahotanni sun rawaito shugaban na cewa, shirin zai ƙarawa al´ummar ƙasar ikone dangane yadda ake mulkarsu.