1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar hakin bil Adama ta MDD ta fara taron ta kan Darfur

December 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuYB
A cikin wani sako na bidiyo da ya aikewa wani taro na musamman na hukumar dake kula da hakkin bil Adama ta MDD, babban sakataren MDD mai barin gado Kofi Annan ya yi kira da a taimakawa al´umomin yankin Darfur mai fama da rikici dake yammacin Sudan. Mista Annan ya ce dole ne a kawo karshen tashe tashen hankulan da ake fama da su a yankin. Hukumar na gudanar da taron ta yau a birnin Geneva akan halin da ake ciki a yankin na Darfur. A wani labarin kuma MDD ta ba da sanarwar cewa daga wannan mako wasu ´yan gudun hijirar Sudan kimanin dubu 20 zasu fara komawa gida daga kasashe makwabta.