1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta zargi Iran da ci gaba da aikin nukliyarta

Gazali Abdou TasawaAugust 27, 2015

Hukumar Nukliyar ta Duniya ta zargi kasar ta Iran da neman gina wata sabuwar cibiyar gudanar da ayyukan nukliya a asirce dabra da tsohuwar cibiyar Parchin da ta ke shirin bincika.

https://p.dw.com/p/1GN4U
Kernkraftwerk Iran
Hoto: picture alliance / abaca

Hukumar kula da makamashin nukliya ta duniya wato IAEA ta zargi kasar Iran da ci gaba da gudanar da ayyukanta na Nukliya a asirce tun a cikin watan Mayun da ya gabata.

A cikin wani rahoto da ta fitar a asirce dangane da binciken da ta ke yi a cibiyoyin sojin kasar ta Iran da ka iya aiwatar da shirin nukliya da amma kuma ya fada hannun kamfanin dillacin labaran Reuters ,hukumar ta IAEA ta ce wasu hotuna da tauraren dan Adam dinta ya dauko sun nunar da kasancewar zirga-zirgar motoci da wasu na'urori dama jigilar kayan gine -gine a cibiyar sojin kasar ta Parchin daya daga cikin guraren da ta ke zargin Iran din na gudanar da ayyukanta na nukliya da kuma yarjejeniyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya ta tanadi bincika.

Idan dai har wannan zargi da hukumar ta IAEA ke yi wa kasar ta Iran ya tabbata to kwa zai kasance babbar barazana ga makomar yarjejeniyar Nukliyar da manyan kasashen duniyar suka cimma da kasar ta Iran a tsakiyar watan Yulin da ya gabata. Sai dai tuni hukumomin kasar ta Iran suka yi watsi da wannan zargi wanda suka ce ba shi da tushe.