1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta ce an sami ƙarin mutane 5 da suka rasa rayukansu a ƙasar Indonesiya, sakamakon kamuwarsu da murar tsuntsaye.

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buy1

Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta tabbatad da cewa, an sami ƙarin mutane 5 da suka rasa rayukansu a ƙasar Indonesiya, sakamakon kamuwarsu da ƙwayoyin cutar nan H5N1 na murar tsuntsaye, abin ya da kawo yawan waɗanda cutar ta halaka, zuwa 30 a ƙasar. Rahotannin da suka iso mana daga birnin Jakarta, sun ce, ban da Vietnam, yanzu Indonesiya ce ƙasa a jeri na biyu a duniya, inda aka fi samun yawan mace-macen mutane, sakamakon kamuwarsu da cutar.

Ana dai zargin gwamnatin Indonesiyan ne da rashin ɗaukan isassun matakai, kamar kashe dabbobin, wajen hana yaɗuwar ƙwayoyin cutar, waɗanda a halin yanzu suka shafi jihohi 27 daga 33 na kasar.