1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar lafiya ta gargadi turai game da yaduwar cutar TB

October 10, 2006
https://p.dw.com/p/BugR

Hukumar lafiya ta duniya tayi gargadin cewa nahiyar turai tana fuskantar barazanar yaduwar cutar tarin fuka mafi muni tun yakin duniya na biyu.

Hukumar tace ana kara samun kwayoyin cutar ta TB wadanda basa jin magani.

Cikin kasashe 20 dake dauke da mafi yawan kwayar cutar da bata jin magani,kasashe 14 suna a gabashin turai da kuma tsakiyar asiya.

Hukumar lafiya ta duniya tare da wasu kungiyoyin kula da lafiya 20 sunyi gargadin cewa cutar zata iya bazuwa zuwa yammacin turai,saboda haka sunyi kira ga gwamnatoci da su kaddamar yekuwar sanarda jamaa kafin cutar tafi karfin mutane.

Kusan mutane 500,000 suke kamuwa da cutar TB a turai da tsakiyar asiya a kowace shekara,70,000 kuma suke mutuwa sakamakonta.

Rahotannin sunce a duk duniya baki daya kuma mutane 5,000 suke mutuwa a kowace rana sakamakon cutar ta TB