1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar NBC ta dakatar da kamfanin sadarwa na DAAR a Nigeria

October 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvO2

Mahukuntan Nigeria sun bayar da sanarwar dakatar da hukumar sadarwa ta DAAR dake mallakar gidan talabijin na AIT da gidan rediyon FM na Raypower a matsayin wucin gadi.

A cewar hukumar dake kula da kafafen yada labaru ta kasar wato NBC, an dauki wannan matakin ne bisa labarai masu sabani da juna da suka bayar a game da hatsarin jirgin saman nan na Belveiw.

Sanarwar ta NBC taci gaba da cewa yanayi na yadda gidan talabijin din na AIT ya bayar da labarin hatsarin ya saka da yawa daga cikin kafafen yada labaru na kasashen ketare cikin hali na rudani game da yadda suke bayar da labarun halin da ake ciki.

Bugu da kari ba a da bayan haka, hukumar ta NBc ta kuma soki lamirin kafafen yada labaru na kasar gaba dayan su game da yadda suka bayar da labarai na abin da ya faru ga hatsarin jirgin na Belveiw.

A waje daya kuma hukumar zartarwa ta kamfanin na DAAR tace a shirye take ta kare wannan zargi da ake mata, domin labarin data bayar babu wani sabani a cikin sa. To amma duk da haka hukumar ta DAARR tace zata bi umarnin hukumar ta NBC har zuwa lokacin da za a warware wannan rikici.