1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar shari’ar Isra’ila ta yi kira ga shugaban ƙasar da ya yi murabus.

October 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bue1

Antoni-janar, na ƙasar bani Yahudun Isra’ila, ya shawarci shugaban ƙasar Moshe Katsav, da ya yi murabus daga muƙaminsa, yayin da ake gudanad da bincike kan zargin aikata laifin fyaɗe, da ake yi masa. Gidan rediyon Isra’ilan ya ruwaito cewa, Antoni-Janar ɗin ya yi kiran ne, a lokacin da yake masa tambayoyin wata babban kotun ƙasar a kan wannan batun. Hukumar ’yan sandan ƙasar dai ta ce tana da hujjojin da ke jiɓinta shugaba Katsav da zargin fyaɗe da akke yi masa, ga mata da yawa, ma’aikatan ofishinsa.

A cikin wata sanarwar da ya bayar jiya lahadi, shugaban Isra’ilan ya ce ba zai yi murabus ba, kuma ya dage fes, kan ba shi da wani laifi.