1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar Turai za ta shiga tsakanin Rasha da Ukrain kan batun iskar gas

January 1, 2006
https://p.dw.com/p/BvE8

Russia/Ukraine

Rasha tace nan da ,wani dan lokacine zata dakatar da baiwa kasar Ukraine iskar gas saboda Ukraine din taki ta amince da sharadin da rashan ta gindaya mata game da cinkin gas din dake tsakaninsu.

Matakin dai ya biyo ,bayan waadin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya baiwa tsohuwar kasar ta gamayyar tarayyar Soviet din ne zuwa karfe goma sha biyun daren jiya na ta amince da sabuwar yarjejeniyar sayar mata da gas din,wadda a karkashin ta Rasha zata cigaba da saida mata da gas din akan tsohon farashi har zuwa watan Aprilu na wannan sabuwar shekara wanda daga nan kuma zata rinka saida mata a kan farashin kasuwar turai,linki hudu akan farshin na yanzu.

Rashandai tace da safiyar nan ne dai karfe bakwai na GMT kamfanin gas dinta Gazprom zai dakatar da aikawa Ukraine din gaz din inhar bata amince da sabon tsarin ba.

Rashan dai tace kasashen Turai da ke samun iskar gas dinnata ta bututun da ya bi ta Ukrain din irinsu Hungary da poland ba zasu gamu da matsala ba,amma tun kafin aje koina kasar Poland tace karfin iskar da take samun ya yi kasa.

Dngane da wannan dambarwane dai kungiyar gamayyar turai ta umarci kwamitin ta mai lura da harkokin da suka shafi iskar gas da ya shiga tsakanin Rashan da Ukrain don sasanta lamarin.