1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zartaswa ta KTT ta gabatar da shawararta game da karbar Turkiyya a kungiyar

October 6, 2004

Bayan shekaru 40 na gwagwarmayar neman shigowa inuwar KTT a yau hukumar zartaswa ta kungiyar ta ba da shawara game da karbar Turkiyya a gamayyar ta kasashen Turai

https://p.dw.com/p/Bvft
P/M Turkiyya Erdogan
P/M Turkiyya ErdoganHoto: AP

A yau laraban nan ne kantoman hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai akan manufofin karbar karin kasashe Günter Verheugen ya gabatar da shawarar hukumar a game da karbar Turkiyya, wacce ta tanadi wata manufa tayin sara tare da duban bakin gatari, bayan kai ruwa ranar da wakilan hukumar zartaswar su kimanin 30 suka sha famar yi akan wannan batu. A lokacin da yake bayani game da haka Verheugen cewa yayi:

Mun cimma daidaituwa mai ma’ana saboda amincewar da muka yi cewar tsarin dokokin kasar Turkiyya yayi daidai da na sauran kasashen kungiyar tarayyar Turai, sai dai kawai ana fama da tafiyar hawainiya wajen aiwatar da wadannan dokoki a kasar.

Wato dai a takaice kasar Turkiyya ta cimma wani matsayi ne mai gamsarwa a game da sharuddan siyasar da aka shimfida mata a taron kolin shuagabannin kasashen KTT da aka gudanar a Kopenhagen misalin shekaru biyu da suka wuce. Hukumar zartaswa ta kungiyar tayi bayani filla-filla a game da gibin da kasar ke fama da shi, kuma ba za a saduda da matakan keta haddin dan-Adam da azabtar da fursinonin dake faruwa a tashoshin ‚yan sandan kasar ba. Shugaban hukumar zartaswar Romano Prodi ya yaba da irin ci gaban da Turkiyya ta samu a cikin hamzari as matakanta na garambawul sannan ya ce karbar Turkiyyar mai rinjayen Musulmi a tsakanin al’umarta zai taimaka wajen bunkasa manufofin tsaron nahiyar Turai ta la’akari da muhimmancin kasar a bangaren tsaro. A dai wannan halin da ake ciki yanzu ba wanda ya san yadda al’amura zasu kaya a kasar ta Turkiyya a cikin shekaru 10 ko 12 masu zuwa. A sakamakon haka aka tanadar da wani babin dake ba da damar dakatar da shawarwarin karbar kasar idan har zarafi ya kama, in ji Günter Verheugen. A cikin shawarar da ta bayar hukumar zartaswar ta KTT bata tsayar da wata rana domin fara shawarwari da kasar ta Turkiyya ba tana mai danka alhakin lamarin akan shugabannin kasashen kungiyar a lokacin taron kolinsu na watan desamba mai zuwa. A baya ga kasar ta Turkiyya hukumar zartaswar kazalika ta ba da shawarwarinta dangane da ci gaban da sauran kasashen dake neman shigowa kungiyar suka samu. Bisa ta bakin Verheugen kasashen Rumaniya da Bulgariya sun samu ci gaba matuka ainun kuma ana iya sanya hannu akan takardun yarjeniyoyin karbarsu a kungiyar. kamar yadda aka tanadar a shekara ta 2007, a shekara mai zuwa. To sai dai kuma dukkan kasashen biyu na fama da tafiyar hawainiya wajen yaki da cin hanci. Tilas ne kasar Bulgariya ta kyautata matsayin rayuwar ‚yan kabilar Roma tsiraru sannan ita kuma Rumaniya wajibi ne ta dakatar da fataucin mata a kasar. Muddin kasashen ba su cimma nasarar manufofin garambawul da ake bukata ba tilas a daga manufar karbar tasu har tsawon shekara daya.