1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Habasha sun yi belin wasu daga mutanen da su ka tsare a kurkuku

November 16, 2005
https://p.dw.com/p/BvKv

A Habasha gwamnati ta yi belin mutane 754 daga wanda ta kama a cikin zanga zangar da ta gudana, a kwanaki baya wace kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 42.

Cemma a jiya, hukuma ta bayana sallamar mutane kimanin dubu 4.

A jimilce ya zuwa yanzu, jami´an tsaro sun sako mutane fiye da 9000, da su ka tsare tun bayan zaben yan majalisar dokoki na ranar 15 ga watan Mayu na wannan shekara.

Gwamnati har yanzu,ba ta bayyana yawan mutanen da ke tsare ba a kurkuku, saidai kungiyoyin kare hakokin bani adama da jikadodin kasashen ketare, na nuni da cewa za a samu yanzu haka dubbunan mutane, da gwamnati ta kama.

Daga cikin wanda a ka sallama tsakanin jiya da yau, babu shugabanin jam´iyun adawa, da yan jaridar da a ka kama.

A game da yan adawar a makon da ya wuce, idan ba a manta ba, Praministan Habasha Meles Zenawi yace za a gurfanar da su gaban kotu, tare da zargin su da cin amanar kassa.

Wannan lefi kuwa, ya na iya jawo masu hukunci kissa.