1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin sojin Niger sun tsare wasu tsoffin Ministoci.

March 29, 2010

Gwamnatin mulkin sojin Niger ta tsare wasu Ministocin tsohuwar gwamnatin Tanja Mamadou.

https://p.dw.com/p/Mh85
Tsohon shugaban ƙasar Niger Mamadou Tandja.Hoto: AP

Hukumomin Sojin a Nijer sun tsare wasu tsoffin Ministocin Gwamnatin tsohon shugaba Mamadou Tandja. Kafofin jami'an tsaro a Nijer, sunce an kama tsoffin Ministocin ne bisa zargin da ake masu da neman yin zagon ƙasa ga sabuwar gwamnatin. Kanfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito Ministan cikin gidan Nijer Ousmane Cisse , yana cewa tsoffin Ministocin da yanzu haka suka shiga hannun sun haɗa dana kuɗi Ali Lamine Zene dana Shari'a Garba Lompo da kuma wasu daraktocin kanfanonin Gwamnati da dama. Wannan dai shine karon farko da hukumomin Sojin ta Nijer da suka kifar da gwamnatin Tanja, suka kame wasu manyan Jami'an tsohuwar Gwamnatin bisa zargin aikata ba dai- dai ba. Har yanzu dai Tsohon Shugaba Mamadou Tandja na tsare a hannun hukumomin. 

Mawallafi : Babangida Jibril

Edita        : Abdullahi Tanko Bala