1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Tchad sun ƙi amincewa da karɓar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a iyakar su da Sudan

March 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuQu

Hukumomin ƙasar Tchad, sun bayyana adawa ga rundunar kwantar da tarzoma da Majalisar Ɗinkin Dunia ke bukatar aikawa, a iyakar Tchad, da yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Sanarwar da fadar mulkin NDjamena ta hiddo, ta nunar da cewa, a maimakon rundunar sojoji, Tchad na iya amincewa da tawagar yan sanda, domin su kulla da tsaron yan gudun hijira.

Sanarwar ta zo kwastam! ga jami´an diplomatia, domin shugaba Idriss Deby da kan sa, ya bayana amincewa da karɓar rundunar ta Majalisar Dinkin Dunia, albarkacin ziyara aikin da Praministan Ministan France, Dominique de Vilepin ya kai Tchad, a watan november, na shekara ta 2006.

A watan Februaru da ya gabata, Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, tunni, har ya yanke shawara aika dakaru dubu 6, zuwa dubu 10, a iyakokin ƙasashen Tchad, da Jamhuriya Afrika ta tsakiya, da kuma Sudan, da zumar hana yaɗuwar matsalolin yankin Darfur .