1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci kan kashe-kashe a Côte d'Ivoire

Mouhamadou Awal Balarabe
April 14, 2017

An yanke wa Janar Brunot Dogbo Blé na côte d'Ivoire hukuncin shekeru a gidan yari 18 bisa laifin kashe-kashe lokacin da kasar ta yi fama da rikicin siyasa a 2011.

https://p.dw.com/p/2bE3l
Elfenbeinküste General Brunot Dogbo Ble
Hoto: Getty Images

Wata kotun kasar Côte d'Ivoire ta yanke wa tsohon dogarin fadar shugaban kasa hukuncin daurin shekaru 18 a gidan yari, bayan da ta sameshi da hannu wajen sace mutane hudu tare da kashesu a lokacin da kasar ta yi fama dsa rikicin siyasa a shekara a 2011. Shi dai Janar Brunot Dogbo Blé ya kasance shugaban rundunar da ke kare shugaba Laurent Gbagbo lokacin da satar mutanen hudun ciki har da 'yan faransa biyu ta faru a otel Novotel na Abidjan.

Su ma mataimakan hapsan sojan na Côte d'Ivoire guda biyu, an yanke musu hukuncin shekaru 18 a kan wannan batu, yayin da kotun ta yanke wa wani babban jami'in 'yan sanda mai suna Osée Loguey hukuncin shekaru 20 a gidan yari bisa laifin aiwatar da kashe-kashen wadanda suka sace.

A ranar 4 ga watan Afirilun  2011 ne wani sojen kundumbala ya kutsa harabar otel Novotel na Abidjan, inda ya kama shugaban otel din da mataimakansa uku. Binciken da aka gudanar ya nunar da cewar anta azabtar da su a fadar shugaban Côte d 'Ivoire kafin a kashesu.