1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci saboda kisa a Berlin

April 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6x

Germany

A yau ne wata kotu anan jamus ta yankewa wani mutumin Turkiyya hukuncin daurin shekar 9 da rabi a gidan yari,saboda samunsa da laifin kisan gilla wa yar uwarsa.Kisan gilla da akayiwa Baturkiya Hatun Surucu mai shekaru 23 da haihuwa ,ayayinda take jiran mota a wata unguwa dake birnin Berlin a shekarar data gabata dai,ya haifar da mahawara tsakanin musulmi baki masu tsattsauran raayi da alummar jamusawa.Wannan mata dai ,tun tana yarinya aka mata auren tilas da dan uwanta a Turkiyya ,kana daga baya ta samu tserewa daga yan uwanta dake zaune a Berlin,inda ta kama gida tana zaune da danta mai shekaru 5 da haihuwa,batu da yan uwan suke ganin cin mutunci ne a bangarensu.Kaninta,Ayhan Surucu, ya amince da harba bindigan daya kashe Hatun,a gaban kotu,wanda ya jagoranci hukuncin daurin shekaru 9 da watanni 3 a gidan wakafi,domin lokacin da ya aikakata laifin a bara ,shi yaro ne,shekarunsa basu kai hukuncin manya ba.