1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HUKUNCIN DAN KUNGIYAR AL-TAWHID A JAMUS

ZAINAB AM ABUBAKARNovember 26, 2003
https://p.dw.com/p/BvnQ
Kotun garin Dusseldof anan jamus yau ta yankewa Shadi mohammad Mustapha Abdellah dan kasar Jordan mai shekaru 27 da haihuwa hukuncin daurin shekaru 4 ,saboda kasancewa a kungiyar masu tsatssauran addinin Islama na na al-Tawhid,wanda jamian leken asirin kasannan sukace reshen kungiyar Alqaeda na Osama bin Laden ne.An kama Abdellah da laifin shirin kaiwa wasu wuraren shakatawa guda biyu na yahudawa a Dusseldorf hari, tare da wata cibiyar ingantan alumman yahudawa dake da sansani a Berlin.
Abdella ya amince da dukkan zargi da aka masa ,wanda ya sa masu gurfanar dashi suka bukaci ayanke masa rabin hukuncin da zaa zartar a akansa na shekaru goma a kurkuku.
Bayanan daya gabatar a gaban kotun dai ya taimaka wajen bawa masu binciken yadda kungiyoyi masu tsattsauran raayi dake nan jamus ke tafi da ayyukansu.Bugu da kari Abdellah ya kuma bada shaida akan wasu yan kasar Morocco biyu da ake zargi da hannu cikin harin 11 ga watan satumba da aka kaiwa Amurka a shekara ta 2001,a garuruwan Hamburg,da kuma arewacin jamus.A shekara mai zuwa zai kuma bayyana gaban kotu a matsayin mai bada shaida na masu gurfanar da kara akan wasu yan kungiyar al-Tawhid guda hudu.
Kamar dai yadda jamian tsaro a nan jamus suka sanar,shugaban wannan kugiyar shine Abu Mussab al-Zarqawi,wanda Amurka ta danganta da tsohon shugaban Iraki Sadam Hussein da kungiyar Alqaeda mallakar Osama bin Laden,wanda kuma akace ya jagoranci horor da yan kungiyar a Herat dake Afganistan a karshin bin Laden. Abdellah dai ya shaidawa kotu cewa shima ya karbi horo a a karshin alqaeda,kuma ya kasance daya daga cikin masu tsaron bin Laden na makonni biyu.Bugu da kari yace yasan Ramzi al-Shaiba,wanda ake zargi da harin kunar bakin wake da akayiwa Amurka,wanda kuma ake kann nema ruwa ajallo.
Abdella ya kuma bayayanwa kotun yadda aka masa horon amfani da makamai,boma bomai tare da shirya yadda zaa kai hari.Yace Zarqawi ne ya basu umurnin kai hari wa sansanonin yahudawa guda uku anan jamus ,bayan harin New york da Washinton daya kashe akalla mutane dubu 3.Masu kai kara sunce an rataya masa nauyin nemo wuraren daya dace akai hari ,tare da samo makamai.Harin dake nan baa samu kaiwa ba saboda an cafke shi adai dai wannan lokacin. Hukumomin Jamus wadanda suka fara lura da kungiyar ta al-Tawhid tun daga shekarata ta 1997,sun fara binciken kungiyar ne a watan oktoban 2001,wata guda bayan hare haren na Amurka.Ayayinda shima kuma Abdellah aka kama shi a watan Afrilun 2002.
To sai dai likitoci sun tabbatar dacewa Abdellah na fama da tabuwan hankali,wanda kullun yake cikin maye da gidajen shakatawa,zai kasance abu mawuyaci a tabbatar da bayanan dayayi a gaban kotu,tunda bai mallaki hankalinsa ba.