1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa akan Sadam

December 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuWI

Hukumomin Iraki su bayyana cewa zartarwar kotun daukaka kararaki,adangane da hukuncin kisan da akayiwa Sadam hussein,shine matakin karshe na tabbatar da hukuncin,kuma baa bukatar amincewan shugaba Jalal Talabani.Wannan dai ya kawar da dukkan fata na karshe da ake saran tsohon shugaban Irakin zai samu a hukumance,wanda kuma zai iya tsirar dashi daga wannan hukunci da aka zartar a akansa,saboda laifuffuka daya aiwatar akan bil adama a baya.Ana dai cigaba da smun korafe korafe adangane da wannan hkunci.Ministan harkokin waje na kasar Italia Massimo D,Alema, ya jaddada cewa kungiyar gamayyar turai tana matukar adawa da hukuncin kisa,ayayinda Amurka anata bangare tayi maraba da hukuncin,kamar yadda ake kyautata zato.A ranar 5 ga watan Nuwamba nedai kotun dake sauiararomn shariar tshon shugaban Irakin da mukarrabansa,ta zartar da hukuncinmkiisa akansu,bisa samunsu da klaifin bada umurnin kisan gilla wa shiawa 148 a kauyen Dujail dake Irakin.To sai shugaba Sadam ya aikewa jamaar Iraki wasikar cewa,zai gabatar da kanshi domin a rataye shi a matsayin sadazkarwa,tare da kira garesu dasu hada kai wajen yakar abokan adawa.