1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa kan Tarek Aziz

October 26, 2010

Kotin Ƙolin Iraki ta yankewa Tarek Aziz tsofan mataimakin Firayim Minista hukuncin kisa

https://p.dw.com/p/PoJb
Tarek AzizHoto: AP

Kotun ƙolin ƙasar Iraki, ta yanke hukuncin kisa ga Tarek Aziz, tsofan na hannun damar Saddam Hussain.Kotun ta ce ta same shi da hannu a cikin kisan kiyasu akan ´yan ɗarikar Shi´a a shekara 1991, a yayin da su ka shirya zangar-zangar nuna adawa ga shugaban ƙasa Saddan Husain.A shekara 2003 Tarek Aziz ya miƙa kansa ga sojojin Amurika, bayan sun kifar da mulkin  Saddam Hussain.

Wannan hukuncin ya biwo bayan wani na ɗaurin shekaru 15 a kurkuku da wata kotu ta yankewa Tarek Aziz shima bisa lefin kisa.

A lokacin mulkin Saddan Hussain, Aziz ya riƙe muƙamin mataimakin Firayim Minista da kuma ministan harakokin wajen Iraki.

Ƙungiyar Tarayya Turai ta bayyana adawa ga hukuncin kisan da kotu ta yankewa Tarek Aziz.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu