1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa kan wani malamin Shi'a

Ahmed SalisuJanuary 2, 2016

Hukumomi a Saudi Arabiya sun ce sun kaddamar da hukuncin kisa kan wani sanannen malamin Shi'a Nimr al-Nimr da wasu mutane 46.

https://p.dw.com/p/1HX8r
Saudi-Arabien Protest gegen Hinrichtung Nimr al-Nimr
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A shekarun da suka gabata ne dai kotu ta yanke wa wadannan mutane hukuncin na kisa bisa samunsu da aikata laifuka da suka danganci ta'addanci, kuma baya ga Mr. Nimr da wasu mutane uku, sauran wanda aka kashe din 'yan kungyiar nan ce ta Al-Qaida.

An dai zartar da wannan hukunci ne a gidajen yari na wasu birane 12 na kasar, inda aka harbe wasu yayin da wasu kuma aka fille musu kawunansu.

Tuni dai Iran ta nuna rashin jin dadinta da wannan hukunci da aka zartar musamman ma dai kan Nimr al-Nimr, yayin da mabiya tafarkin na Shi'a a ciki da wajen kasar suka yi zanga-zanga ta nuna rashin amincewa da kisan.