1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta yanke hukunci kan tekun China

Yusuf Ibrahim/YBJuly 12, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahukuntan na Chiana da su mutunta hukuncin domin gujewa taashe-tashen hankalu a yankin.

https://p.dw.com/p/1JNr8
China Präsident Xi Jinping zu Besuch in Serbien
Shugaba Xi Jinping na ChinaHoto: picture-alliance/dpa/K. Sulejmanovic

Kotun da ta saurari karar takaddama da ake yi a tsakanin kasashen da ke da iyaka da tekun Kudancin China ta bayyana cewa mahukuntan kasar ta China ba su da iko na ci gaba da mamayar yankin tekun na Kudancin Sin, kuma ma ko da a tarihi ba ta da iko na mallakar wannan yanki. Har ila yau wannan kotu da ke a birnin Hague ta kara da cewa abubuwan da kasar ta China ke yi na mamayar, musgunawa ce ga mahukuntan kasar Pilipin. Tuni dai mahukuntan na Beijing suka bayyana hukuncin da zama cin fuska a gare su.