1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hulɗar dangantaka tsakanin Amirka da Syria

February 17, 2010

Amirka ta maida hulɗar jakadanci da Syria amma tace takunkumin da ta ƙaƙaba mata suna nan daram.

https://p.dw.com/p/M3kv
Shugaban Amirka Barack ObamaHoto: AP

Shugaban Amirka Barack Obama a wani jawabi da yayi ya baiyana cewa abu na farko da zai yi domin ciyar da yunƙurin diplomasiyya gaba a yankin gabas ta tsakiya shine nuna hasken buƙatar dake akwai na tattaunawa da ƙasashen Iran da Syria.

Tun farkon hawa mulkinsa a matsayin shugaban ƙasa Obama ke neman hanyoyin da zai ƙarfafa wannan dangantaka. Yayin da lamarin dangantakar ya faskara da mahukuntan Tehran a waje guda an sami sassaucin matsayi da birnin Damascus wanda hakan ya sa Jakadan Obama a gabas ta tsakiya George Mitchell kai ziyara har sau uku ƙasar Syria. A baya baya nan mataimakin sakataren harkokin wajen Amirka Nicolas Burns shima ya bi sahun wajen kai makamancin wannan ziyara domin ganawa da shugaban Syria Bashar al Assad. A cewar Samir Seifan mashawarci kan harkokin kasuwanci da siyasa a Damascus dangantaka tsakanin Amirka da Syria abu ne mai faída.

" Amirka ita ce jigo idan babu ita, babu mai iya shimfiɗa wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Babban burin Syria shine dawo mata da yankinta na Tudan Golan da Israila ta mamaye tun shekarar 1967. Tattaunawa da dama da aka yi ta yi sun ci tura tun bayan da baki ɗayan shirin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ya shiga mawuyacin yanayi. A yanzu Amirka da Syria na fatan sauya wannan yanayi.

Symbolbild Reformen in Syrien, Assad und Symbol für Wendepunkt
Shugaban Syria Bashar al AssadHoto: AP / DW

" Syria a shirye take ta cigaba da tattaunawar zaman lafiya da Israila, kuma ta sha nanata hakan sau da dama, amma Israila bata niyya, saboda haka wannan shine muhimmin batu a yanzu tsakanin Syria da Amirka.

Shugaban Amirkan dai na son ganin an sami nasara a shirin zaman lafiyar gabas ta tsakiya. Ƙasar Syria ga magabacin Obama wato George W Bush ya ɗauke ta ne a matsayin shaiɗaniyar ƙasa. Tuni dai Obama ya ɗauki matakin samar da zaman lafiya a Lebanon tare da aniyar taimakawa samun daidaito a Iraqi da warware sarƙaƙiyar rikicin dake tsakanin Israila da Falasɗinawa. A yanzu dai bayan tsawon shekaru biyar Amirka ta baiyana sake tura jakadanta ƙasar domin maida huldar diplomasiyyar dake tsakanin su.

Tshon shugaban Amirka George W Bush ya janye jakadan ƙasar ne daga Syria a shekarar 2005 bayan kisan gillar da aka yiwa tsohon Firaministan Lebanon Rafik Hariri bisa zargin cewa Syria tana da hannu a wanna  kisan.

A yanzu dai sabon jakadan da Obama ya naɗa a ƙasar ta Syria shine Robert Ford wanda ake yiwa kallon ƙwararare ne a yankin, kafin naɗin nasa shine muƙaddashin jakadan Amirka a Bagadaza. Yana kuma jin harshen larabci sosai. Jamiai a ƙasar Syrian na fata zuwa jakadan zai sauya fasalin alámura kamar yadda Samir Seifan mashawarci kan harkokin kasuwanci da siyasa a Damascus yayi bayani.

" Muna fatan karɓar sabon jakadan Amirka a Damascus nan ba da jimawa ba. Akwai abubuwa da dama an yi alƙawura da kuma yunƙuri da dama amma har yanzu babu wani sauyi mai maána da muka gani. Sai dai kuma a cewar Amirka sake maida hulɗar jakadanci da ta yi da Syria ba yana nufin ɗage mata takunkumi bane, waɗannan takunkumi suna nan kuma zasu cigaba.

Mawallafa: Leidholdt, Ulrich/ABdullahi Tanko Bala Edita: Yahouza Sadissou Madobi