1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ASEM Abschluss

October 5, 2010

Shugabannin ƙasashen Asiya da na Tarayyar Turai sun gudanar da taron ƙarfafa hulɗar tattalin arziki tsakaninsu

https://p.dw.com/p/PW6a
Shugabannin EU da na Asiya a taron BrusselHoto: AP

Taron ƙasashen Asiya da na Tarayyar Turai ya buƙaci da a ɗau ƙwararan matakai na warware rigingimun siyasa da suka zamewa duniya alaƙaƙai. Kama daga siyasar ƙasashen Myanmar da Iran da ma rikicin Palasɗinawa da Yahudawa.

Taron wanda ya samu hallartan shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai wato EU 27 da takwarorinsu 19 daga Asiya, wanda suka haɗa da ƙasashe masu ƙarfin faɗa aji a duniya, kamar su China da Indiya da Faransa da Jamus. Shugabannin sun yi tir da ci gaba da gina matsugunan Yahudawa, wanda Isra'ila ta ke yi a yankunan Palasɗinawan da ta ƙwace. Inda shugabannin sukace hakan wani babban targaɗe ne ga tattaunawar samar da zaman lafiya da aka fara.

Da take jawabi kan hulɗa tsakanin ƙasashen EU da Asiya, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace

"Muna godiya ga Asiyawa kan yadda suka agaza, wajen bunƙasa tattalin arzikinmu. Munyi matuƙar juriya a lokacin da aka shiga rikicin tattalin arziki, da aka samu daga Turai da Asiya"

Shugabannin sun kuma buƙaci gwamnatin Myanmar da ta gudanar da zaɓen da ta tsara yi a watan gobe cikin gaskiya da adalci, kana ta saki 'yan siyasan da ke ɗaure a gidajen maza. Inda suka ce sakin 'yan siyasan zai baiwa zaɓen ƙasar ƙarin inganci.

A kan batun ƙara darajar kuɗin ƙasar China wanda ya ɗauki hankalin taron, firai ministan China Wen Jiabao ya yi ƙarin haske, inda yace.

NO FLASH Merkel in China Wen Jiabao
Angela Merkel da Wen JiabaoHoto: picture alliance/dpa

"Dole mu warware tambayoyin da ke kawo sarƙaƙiya, waɗanda suka shafi darajar kuɗinmu. Wannan abune mai mahimmanci ga makomar tattalin arzikinmu"

Shi kuwa shugaban babban bankin ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro Jean-Claude Juncker, yace idan al'amura suka dai-daita ko wane ɓangare zai samu riba.

"Muna tunanin cewa idan aka ɗaga darajar kuɗin China, to ita kanta Chinar da ma tattalin arzikin sauran ƙasashen duniya zai amfana"

Shugabannin na Tarayyar Turai da Asiya, sun buƙaci da a samar da masalaha kan zaman ɗar-ɗar dake aukuwa tsakanin Koriya ta arewa da ta kudu, inda suka buƙaci koriyoyin biyu da su mutunta ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kan ƙasashen biyu. Kana ya nemi Koriya ta arewa da ta kawar da makaman nukiliyar ta.

Da suka juya kan batun da ya shafi ƙasar Iran, shugabannin sun buƙaci da a ɗau matakin da zai tabbatar da gamsuwar duniya, kan shirin ƙasar na mallakar makamacin nukiliya. Inda suka ce abune mai mahimmanci a samar da mafita kan batun na ƙasar Iran.

Mawallafi: Usman Sheh Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal