1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270910 EU Afrika Partnerschaft

September 28, 2010

Tarayya Turai da Afirka sun shirya zaman taro a Burassels da zumar ƙara danƙon hulɗoɗi tsakanin su

https://p.dw.com/p/POzo
Hulɗoɗi tsakanin Afirka da EUHoto: AP

Wani taron ƙoli tsakanin wakilan ƙasashen Afirka da na EU da ya gudana a Burassels, ya cimma ƙulla hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen nahiyoyin biyu, waɗannan matakan da aka ɗauka sun nuna alamun haɓɓaka manufofin ɓangarorin biyu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙarfafa kiran da ta ke yi ga ƙasashen da suka ci gaba ta fannin tattalin arziki, da su ƙara tallafin da suke baiwa ƙasashe masu tasuwa. Don haka ne ya sa ake ta kira ga ƙasashen da su sanya wannan manufar tun daga kasafin kuɗinsu. To sai dai wani abun takaici shine duk da shekaru aru aru da aka yi ana baiwa ƙasashe masu tasowa tallafi, amma har yanzu basu fita daga ƙangin talauci ba. Abinda kwamishinan raya ƙasashe na EU Andris Piebalgs ya tabbatar:

Taimako babu inda zai kai, idan bamu samu tushen matsalar ba. Idan ba mu bi doka da oda ba, tsaro da kuma kekkyawan tsarin tafiyar da kuɗi, to babu yadda mutane za su tsara rayuwarsu

 Wannan ya sa wasu  ƙasashen na Afirka yin tunanin cewa ƙila za su kai ga tsayawa da ƙafafuwansu, ta yadda za su manta da talauci. To amma Mark Plant jami'i a hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF, ya ce amma dai ba duk ƙasashen Afrika ba:

Ƙasashen da suka samu ci gaba, suna da zaman lafiya ne, daga cikin gida da maƙobtansu. Don haka yanzu nauyi ne kan ƙasashen duniya da su tabbatar da warware tashe tashen hankula da suka addabi nahiyar.

To sai dai shi kuwa kwamishinan tattalin arziki na ƙungiyar ƙasashen Afirka Maxwell Mkwezalamba ya ce samar da zaman lafiya kaɗai ba zai wadatar ba. Ƙasashen Afirka sai sun yi aiki tare domin  ƙarfafa hulɗa tsakaninsu, kamar yadda take a Tarayyar Turai. Ko da yake, yace samu kasuwar bai ɗaya kamar na Turai abune dake da wuya:

Na yi imanin cewa cigaba da makomar Afirka ya rataya ga yadda ƙasashen ke dangataka da juna, da kuma sauran ƙasashen duniya.

A da, ƙasashen Turawa na da ƙwarin gwiwar cewa su suka reni ƙasashen Afirka, kuma kumai zai zo musu da sauƙi, to amma lamura sun sauya, inda yanzu suke gogayya da ƙasashen China da Burazel da Indiya, wajen sayo albarkatun ƙasa da Allah ya horewa Afirka. Kamar yadda Andreas Prosch na ƙungiyar raya ƙasace ta jamus ya bayyana:  Turai ta yi kusan rasa damar da take da shi. Yanzu ƙasashen Afirka na da zaɓi. Kuma ina tunanin hakan zai sa mu sauya halayen mu kan nahiyar Afirka. Ɗaukacin wakilan da su ka yi jawabi a taron, sun ce dole ne Turai ta sauya dangantakarta da Afirka, wato daga ƙasashen da su ke ganin renon su ne, izuwa abokanai kasuwanci. Domin yanzu ƙasashen Afirka na da damar da za su iya fidda kansu daga ƙangin talauci. Kuma wannan shine taro da fayyace gaskiya tun bayan kawo ƙashen mulkin mallaka.

Mawallafi:Usman Shehu Usman

Edita:Yahouza Sadissou Madobi