1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar Jamus da Afirka za ta kara ingantuwa

Daniel Pelz MNA
September 20, 2017

Gwamnatin Jamus ta gabatar da shirye-shirye masu tarin yawa da ke da burin inganta hadin kai da bunkasa harkokin ciniki da kasashen Afirka.Shin ko yaya batun yake a yakin neman zaben majalisar dokokin Jamus?

https://p.dw.com/p/2kNCg
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/A. Weigel

A wannan karon ma Afirka ba ta dauki hankali ba a kan allunan yakin neman zabe. Batutuwan cikin gida kamar inganta rayuwar jama'a da tsaron cikin gida su ne suka fi daukar hankali a yakin neman zabe. To sai dai jam'iyyun ba su kawar da kai daga batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka ba, inji Bernd Bornhorst manazarcin siyasa.

Ya ce: "Za ka yi mamaki idan ka kalli shirye-shiryen zaben za ka ga dukkan jam'iyyun sun yi maganganu daban-daban game da Afirka. CDU ga misali ta yi maganar rage yawan 'yan gudun hijira, The Greens suka ce za su magance matsalar gundun hijira tun daga tushe. Wato an hada batun gudun hijira da nahiyar Afirka. Saboda haka tambayar ita ce shin da gaske suke wajen taimaka wa Afirka ko kuwa kokari suke na nuna wa masu zabe cea za su shawo kan matsalar gudun hijira?" Da ma dai shugabar gwamnati Angela Merkel ta sanya batun nahiyar Afirka zama jigo yayin shugabancinta na kungiyar G20. Kana ministocin gwamnati har guda uku sun gabatar da sabbin tsare-tsaren raya kasa da ke da nufin hadin kai da bunkasa ayyukan zuba jari da ci-gaban tattalin arziki da wasu kasashe biyar na Afirka.

 Martin Schulz jagoran jam'iyyar SPD
Martin Schulz jagoran jam'iyyar SPDHoto: picture-alliance/dpa/J.Büttner

Amma masu sukar lamiri sun ce kawo yanzu ba bu wani abin a zo a gani da aka samu, hasali ma kamfanoni Jamus ne za su fi cin gajiyar sabbin matakan, zargin da Andreas Lämmel shugaban kwamitin kula da hadin kai da Afirka na bangaren jam'iyyar CDU a majalisar dokoki ya ce ba shi da tushe. Ya ce: "Na yi amanna cewa za a iya magance matsalar talauci idan muka kara yawan jari da kamfanoni masu zaman kansu ke yi. Gwamnati ita kadai ba za ta iya magance matsalar ba. Shekaru aru-aru ke nan muke ba da taimakon raya kasa, amma har yanzu kasar ba ta rayu kamar yadda muke so. Saboda haka nake ganin akwai muhimmiyar rawar da kamfanoni masu zaman kansu za su taka a wannan fanni." Ita ma a nata bangaren jam'iyyar SPD ta yi takatsantsa kan wannan batu. Gabriela Heinrich ita ce mataimakiyar kakakin SPD a bangaren ayyukan taimakon raya kasa a majalisar dokoki

Ta ce: "Idan aka tallafa tare da ba wa kamfanoninmu tabbaci, abin da muke ganin yana da alfanu, to mun yi imani za su iya zuba jari da yawa a bangarori da dama a Afirka, inda za su samar da aikin yi tare da ba wa mutane damarmakin samun kudin shiga na tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum."

Su ma sauran jam'iyyun irinsu The Greens da Linke na masu ra'ayin cewa dole a kamanta adalci a harkokin cinikaiya tsakanin Turai da Afirka. Su ma jam'iyyun FDP da AfD da bisa ga dukkan alamu za su samu gurbi a majalisar dokoki bayan zaben na bana, sun goyi da bayan inganta huldar dantgantaku tsakanin nahiyar Turai da nahiyar Afirka mai makwabtaka da Turai, musamman a fannin tsaro.