1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HULDODI TSAKANIN INDIYA DA PAKISTAN A LOKACIN ZABEN KASAR INDIYA.

YAHAYA AHMEDApril 19, 2004

Daga ran 20 ga watan Ifrilu ne za a fara zaben Majalisar Dokoki a kasar Indiya. Bisa dalilan da ke da jibinta da halin tsaro, ba a rana daya ce kawai za a yi zaben a duk fadin kasar ba. Za a yi ta zaben ne a yankuna daban-daban har zuwa ran 10 ga watan Mayu. A halin yanzu dai, jam’iyyar BJP ta Firamiya Atal Behari Vajpayee ce, wani bincike ke nuna cewa, tana da alamun lashe zaben. Sassaucin tsamarin da aka samu tsakanin Indiya da Pakistan, na cikin ababan da Firamiyan ke alfahari da shi a yakin neman zabe. Amma ko yaya wannan sakin jiki tsakanin abokan gaban biyu zai kasance a lokaci mai tsawo ?

https://p.dw.com/p/BvkY
Firamiyan India Vajpayee da shugaba Musharraf na Pakistan.
Firamiyan India Vajpayee da shugaba Musharraf na Pakistan.Hoto: AP

A shekarar 1947, shahararren dan kasar Indiyan nan Mahatma Ghandi, wanda ya jagoranci `yan kasar wajen gwagwarmayar neman `yanci daga Ingila, ya nuna bacin ransa ainun ga rabuwar da kasar ta yi. Gurinsa ne dai ya cim ma samar wa kasar baki daya `yancin kai, inda kuma duk al’ummominta za su sami hadin kai da zaman lafiya. Amma ba haka lamarin ya kasance a watan Agusta na shekarar 1947 ba. Maimakon kasar Indiya da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka ta kasance kasa daya, mai `yancin kanta, sai aka sami rabuwar wannan harabar da Ingila ta yi wa mulkin mallaka zuwa sassa biyu, wadanda kuma daga bisani suka zamo kasashen Indiya da Pakistan. Daga bisani ne kuma, jama’a suka yi ta yin kaura daga kasashen biyu, abin da ya janyo wani mummunan tashin hankali tsakanin musulmi da mabiya addinin Hindu. Kusan dai mutane miliyan daya ne suka rasa rayukansu a wannan rikicin. Mahatma Ghandi, ya bayyana takaicinsa da abin da ya wakanan ne da cewa:-

"Mun sha yin gwagwarmaya, mun ba da kaimi wajen nuna matukar daddagewa ta hannunka mai sansda, ga `yan mulkin mallaka. Amma ga shi yanzu muna kaunar Muntasar a Dawanau. Hakan kuwa ba daidai ba ne. Duk da cewa muna da addinai daban-daban, amma mu duka ai `yan uwa ne, wadanda kuma za su iya rungumar juna."

Duk da adawar da Ghandi ya nuna ga rabuwar kasar dai, jam’iyyar islama ta Mohammed Ali Jinnah, ta cim ma nasarar kaddamad da sabuwar kasa ta Pakistan. Ali Jinnahn da kansa, a lokacin kaddamar da kasar ta Pakistan, ya bayyana cewa:-

"Gurinmu ne mu kasance cikin zaman lafiya a cikin gida da kuma waje. Muna begen kasancewa cikin zaman lumana da kuma kyakyawar hulda da makwabciyarmu – da kuma duniya baki daya."

Wannan zaman lafiyar dai bai tabbata ba. Makwanni kadan bayan samun `yancinsu ne Indiya da Pakistan suka gwabza wani mummunan yaki tsakaninsu, saboda rikici kann yankin nan na Kashmiri. Ban da wannan yakin dai, kasashen sun kuma sake fafatawa da juna har saun biyu.

A cikin shekara ta 2002 kuma, Indiya da Pakistan sun kusan kai ga gwabza wani sabobn yakin kuma, bayan da wasu `yan tsageru suka kai hari a Majalisar dokokin Indiyan a birnin New Delhi. Kai tsaye ne dai, Indiya ta zargi Pakistan da samun hannu a wannan harin. Babu shakka, Pakistan ta yi watsi da wannan zargin. Sai dai, hakan bai magance matsalar ba. A daura da haka, hauhawar tsamari aka samu tsakanin kasashen biyu.

Amma a cikin shekarar bara, a wata ziyarar ba zato ba tsammani da ya kai a yankin Kashmiri, sai Firamiyan Indiya Atal Behar Vajpayee, ya yi wa Pakistan tayin sasanta rikicin da ke tsakaninsu ta hannunka mai sanda. Tun wannan lokacin ne dai kuma, a ka sami sakin jiki a huldodi tsakanin Indiyan da Pakistan. A wani taron kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, Firamiya Vajpayee na Indiya ya bayyana cewa:-

"Kamata ya yi mu nuna kwazo wajen kau da rashin yarda, mu amince da juna, mu fice daga halin rashin jituwa zuwa jituwa, daga tsamari zuwa zaman lafiya."

Tun wannan lokacinm ne dai, kasashen biyu suka shiga shawarwari don sasanta rikice-rikicen da ke tsakaninsu, a cikinsu kuwa har da na yankin Kashmiri. A karo na farko kuma, tun shekaru 15 da suka wuce, wata tawagar kungiyar wasar Krikit ta kasar Indiya, ta yi rangadin wasanni a Pakistan.

Abin tamabya a nan yanzu dai shi ne, wai shin wannan sassaucin tsamari da aka samu tsakanin Indiya da Pakistan, mai dorewa ne ko na wucin gadi ne ? A ganin Kamla Bahsin, wata `yar kasar Indiya mai fafutukar kare hakkin mata da samad da zaman lafiya, sulhunta rikici da samun zaman lafiya, ba a kan takardun yarjejeniya za a iya wanzad da su ba. Ba kuma `yan siyasa, ko sojoji ne za su iya janyo wanzuwarsu ba. Kamar yadda ta bayyanar:-

"Ba Firayiministoci biyu ko shugabannin kasashe biyu ne za su iya samad da zaman lafiya ba. Zaman lafiya zai samu ne kawai, idan miliyoyin jama’a suka shiga tunaninsa, suna bukatar samunsa, sa’annan suna kuma nuna halin zaman lafiya a rayuwarsu ta yau da kullum."