1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Human Rights Watch ya zargi 'yan sandan Faransa

Salissou Boukari
July 26, 2017

Kungiyar kare hakin bil-Adama ta Human Rights Watch, ta zargi jami'an tsaron 'yan sandan na Faransa da amfani da hayaki mai sa kwalla da ke da karfin gaske ga 'yan gudun hijira na Calais.

https://p.dw.com/p/2h9Fy
Frankreich Flüchtlingscamp Dschungel bei Calais wird geräumt
Yadda 'yan sandan faransa ke tarwatsa 'yan gudun hijira a dajin Calais da ke Arewacin kasar.Hoto: picture-alliance/dpa

A cikin rahoton da  ta wallafa a wannan Laraba, kungiyar kare hakin bil-Adaman ta kasa da kasa ta ce amfani da wannan hayaki mai sa kwalla da ake kira "Gaz Poivre" ya kasance abu na yau da kullum da 'yan sandan na Faransa ke ta yi ga 'yan gudun hijira, inda rahoton ya ce daga cikin mutun 61 da aka tambaya, 55 duk sun tabbatar da an taba fesa musu irin wannan gaz mai karfi, yayin da wasu ma suka ce an fesa musu ya fi a kidaya. Sai dai hukumomin na Faransa sun karyata wannan batu. Shi dai wannan gaz ko hayaki mai sa hawaye da ake zargin jami'an tsaron kasar ta Faransa da yin amfani da shi ga 'yan gudun hijiran, na haddasa rashin gani na wani lokaci, tare da sanya ciwon idanu da kuma matsalar numfashi da ke daukan akalla mintuwa 30 zuwa 40 a cewar rahoton.