1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huruci a game da naɗa saban Praminista a Irak

April 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0z

Ƙasashen turai da Amurika, na ci gaba da aika saƙwannin taya murna, ga al´ummomin ƙasar Irak, bayan nasara da su ka cimma jiya, ta naɗa saban Praminista, bayan wattani 4 ,a na ja in ja, tsakanin ɓangarori daban-daban.

Jam´iyun siyasa Irak sun amince da Jawad Al-Maliki, a matsayi Pramista, sun kuma bukaci, ya naɗa ministocin sa, cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Tun bayan kiffar da tsofan shugaban ƙasa, Saddam Hussain, wannan itace gwammnati ta farko, da aka zaba ta hanayar ƙuri´a.

A saƙwan da ya aika, shugaban Amurika Georgse Bush, ya ce wannan mataki, da al´ummar Irak ta cimma, ya zama manuniya, a kan aniyar su, ta shinfiɗa demokardiya mai inganci, da kuma yaƙar ta´adanci.

Bush, ya ce, wannan matakli ne, wanda ke ƙara ƙarfin gwiwa ga Amurika, da abokan ƙawancen ta , da ke aiki, ba dare ba rana, domin tabattar da kwanciyar hankali, da Demokraɗiya a ƙasar Irak.

Sannan ya tabatar wa saban Pramimistan cewar, Amurika, a shire ta ke, ta bashi haɗin kai, domin cimma burin da a ka sa gaba a wannan ƙasa.

Saidai ranar nadin saban Praministan ta yi daidai da mutuwar ƙarin sojoji, 5 na Amurika a cikin hare- hare daban-daban da su ka wakana jiya a birnin Bagadaza.

Daga farkon yaƙin Irak, zuwa yanzu, a jimilce sojoji 2.389 na Amurika, su ka sheƙa lahira.