1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hurucin Gwamnatin Niger a game da yan ƙasar Italia 2 da yan tawaye su ka kama

August 27, 2006
https://p.dw.com/p/BulV

Gwamnatin Jamhuriya Niger, ta bayana cewar yan yawan shakatawar nan 2 na Italia, da wasu mutane su ka capke, a halin yanzu, ba su cikin Niger,suna wata kasa makwabciya, sannan gwamnati na iya ƙoƙarin ta, domin samun belin su.

Ƙungiyar tawayen Fars, wadda da dauki alhakin kamun yan yawan shaƙatawar na ƙasar Italia, ta bayyana aniyar sallamar su, a jiya.

Ya zuwa yanzu,turawa 2 su ka rage ,cikin hannun yan tawayen, daga jimmilar mutane fiye da 20, da su ka kama, ranar litinin da ta wuce,a kudu maso gabacin Jamhuriya Niger.

A cikin sanarwar da su ka hiddo, yan tawayen su yi kashedi, ga yan yawan shaƙatawa, daga turai, su daina sa ƙaffa, Jamhuriya Niger.

Yan tawayen FARS, sun zargi Gwamnatin ƙasar, da rashin mutunta tsarin mulkin demokradiya, da kuma ƙuntatawa jama´a.

Idan dai ba manta ba ƙungiyar FARS na daya daga ƙungiyoyin tawaye, da su ka tada zaune tsaye, a Jamhuriya Niger a farkon shekarun 1990.

An rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lahia, tsakanin gwamnatin Niger, da yan tawayen FARS a shekara ta 1997 bisa jagorancin ƙasar Tchad.

A sanarwar da gwamnatin ta hido, ta ce babu tawaye yanzu cikin ƙasa,ɓarayi ne kaɗai da masu fashi, na fakewa bayan wata tsofuwar ƙungiyar tawaye.