1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

I S ta sake kwace iko da yankuna a Siriya

Abdul-raheem Hassan
November 10, 2017

Kungiyar da ke fafitukar mamaye gabashin kasar, ta samu nasarar sake karbe wasu garuwa a hannun dakarun gwamnati bayan fito na fito da Sojoji a kan iyaka da Iraki.

https://p.dw.com/p/2nQ6X
Syrien Soldaten
Hoto: picture-alliance/AP Photo/SANA

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Sojojin gwamnati suka yi ikirarin mallake yankunan 'yan tawayen, kungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights, ta ce bangarokrin biyu sun gwabza kazamin fada ta hanyar musanyar wuta a Deir al-Zour da ke da arzikin man fetur.

A yanzu 'yan tawaye sun samu damar karbe kashi 40 cikin dari na yankin al-Bu Kamal da ke kusa da kan iyaka da kasar Iraki, to sai dai wannan kwan gaba kwan bayan na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu rahotanni ke nuna bayyanar shugaban kungiyar ta I S Abu al-Baghdadi a a garin Albu Kamal da ke Siriyar.

Amma rahoto da mayakan Hezbollah suka fitar, bai bayyana ko an kama Baghadadi a gumurzun wuta tsakanin mayaka da sojoji a kan iyakar Siriya da Irakin ba.