1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC: Dole Katanga ya biya diyya a Kwango

March 24, 2017

Kotun ICC ta umurci tsohon shugaban 'yan tawaye Germain katanga da biyan diyya ga wadanda 'yan tawaye suka yi wa kisan kiyashi a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/2Ztoq
Niederlande Menschenrechte Germain Katanga vor dem Strafgerichtshof in Den Haag
Hoto: AP

Kotun hukunta manyan laifikan yaki ta duniya ICC ta bada umurunin biyan diyya ga iyalan wadanda aka yi wa kisan kiyashi, a rikicin da ya gudana a wani kauye na Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango a shekara ta 2003. Cikin wani hukunci da ta yanke a wannan Jumma'a da ke zama irinsa na farko cikin tarihi, kotun da ke da mazauninta a birnin The Hague ta kayyade Dollar 250 a matsayin yawan kudin da za a bai wa kowa daga cikin  mutane 297 da abin ya shafa.

Alkalan kotun ICC sun aza wa tsohon shugaban 'yan tawaye Germain katanga da aka yanke wa hukuncin shekaru 12 a gidan yari, nauyin biyan miliyan guda na Dollar Amirka daga cikin miliyan uku da dubu 750 na kudin diyyar.  kimanin mutane 200 ne suka rasa rayukansu a kauyen Bogoro lokacin da masu biyeyya ga katanga suka far musu.

Kotun ta ICC ta bayar da umurnin karbe dukiyar da katanga ya mallaka domin tanadar biyan diyyar kafin ranar 27 ga watan Juni.