1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Idriss Deby da Omar El-Beshir ba su halarci ba taron Dakar

August 10, 2006
https://p.dw.com/p/BunA

Shugaba Idriss na Tchad, da takwaran sa, Omar El Beshr na Sudan, sun ƙi amsa gayatar da shugaban ƙasar Senegal Abdullahi Wade, yayi masu a birnin Dakar, a yunƙurin sasanta rikicin da ke tsakanin su.

Jiya laraba ne a ka tsara cewar, shugabanin za su haɗu a Dakar, tare da mai masaukin baƙi, domin ɗinke barraka da ta kunno kai tsakanin su, bayan da Idriss Deby, ya zargi AL Bashir, da rura wutar rikicin Tawaye a Tchad.

Maƙwabtan 2 masu gaba da juna, sun haɗu iya, a birnin N´Dajmena albarkacin bikin rantsar da Idriss Deby.

A sakamakon ganawar da su ka yi, shugaba Ƙhaddafi na kasar Lybia, ya bayana samun nasara sasanta su.

Wani jami´in ƙasar Senegal,ya zargin Ƙhadafi, da yin ƙafar angullu, ga haduwar ta birnin Dakar, saboda hasada.

A cewar sa ,bayan kasawar da shugaban ƙasar Lybia yayi, na shawo kan wannan rikici, ba shi buƙatar ganin wani ya samu nasara.

Ya zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukunce, da ta hito daga fadar gwamnatocin ƙasashen domin bayyana dalilan da su ka hana wanzuwar wannan taro.