1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ilimin fasaha da tsarin inji mai kwakwalwa ga yara

Sam Olukoya/ NDOctober 7, 2015

A Najeriya kamar a wasu kasashen Afirka an dukufa wajen samar da tsarin ilimin inji mai sarrafa kansa da zai taimaka wa yara su fahimci ilimin fasaha.

https://p.dw.com/p/1Gjt6
Roboter
Hoto: Colourbox

Tsarin inji mai kwakwalwa da ke iya sarrara kansa da ake kira Robot, ta hanyar amfani da na'urar kwamfuta, wani tsari ne da ake son amfani da shi ga tafiyar da tsarin ilimi a mafi yawa daga cikin kasashen nahiyar Afrika. Sai dai hakan bai samu ba sakamakon rashin kayayyakin fasaha. A Najeriya ma ana ta kokarin samar da tsarin wanda kuma zai taimaka wa yara su fahimci ilimin fasaha a nan gaba.

An yi gwajin wani inji mai kwakwalwa da ke iya sarrafa kansa a wata cibiya da ke a jihar Lagos ta Tarayyar Najeriya inda ake koya wa yara yadda za su hada injin.

Fasaha mai muhimmanci ga inganta ilimin yara

Kalu Chidebere Kalu wani yaro dan shekaru 16 da haihuwa da ya kirkiri wannan inji ya bayyana cewar wannan fasahar na da muhimmanci tare da kuma yadda yake gudanar da aikin.

"Kamar yadda ka ga yana tafiya haka zai ta tafiya da kansa ba tare da wani na jan akalarsa ba. A takaice dai da kansa yake iya tafiya, kuma yana tafiya da kayan da ya dauka tare da ajiye su a inda aka umarce shi ya ajiye."

Bildergalerie Tim Burton Ausstellung The World of Tim Burton Brühl Deutschland
Hoto: picture-alliance/dpa/M.Becker

Shi dai wannan shirin manufar ita ce 'yan makarantun gaba da Firamare su samu kwarewa a kansa kuma zai taimaka wa dalibai musamman wadanda suka fito daga gidajen marasa galihu, haka kuma zai iya canja rayuwarsu ta wannan fanni.

Nakaltar ilimin inji mai sarrafa kansa

Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin Okeke Desmond, ya bayyana cewar a shirye yake ya yi amfani da na'ura mai kwakwalwa wajan samar da wani tsari da ake bukata wajan sarrafa inji mai kwakwalwa da ka iya sarrafa kansa.

"Tsintar kaina da na yi a cikin shirin ya bani damar sanin ilimin na'ura mai kwakwalwa sosai, wadda kuma take taka muhimmiyar rawa wajan sanin ilimin. Haka kuma na samu kwarewa a kan siddabarun kwamfuta wanda kuma ya kasance daya daga cikin shika-shikan tsarin."

Desiree Craig wata jami'a ce a cibiyar koyar da shirin ta bayyana cewar tsarin ka iya canja rayuwar yara, wadanda za su yi amfani da abin da suka koya wajan kawo cigaba mai ma'ana a fannin tsarin kimiyya da fasahar Najeriya a nan gaba.

"Ta wannan shirin na sanin ilimin inji mai kwakwalwa da ka iya sarrafa kansa ake kokarin cusa wa yara dalibai wata akida da za ta taimaka ta fannin fasahohin cigaban kasar u kai har ma da duniya baki daya."

Matukar dai al'amarin ya bibiyin yara masu tasowa, Najeriya za ta zama mai alfahari. Abin da kawai ya rage wa kasar shi ne ta yi kokarin dawo da 'yan kasar kwararru ta fannin kimiyya da fasaha da suka yi kaka-gida a kasashen duniya ta yadda za su taimaka mata don cimma burin da aka sanya a gaba.