1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta nemi rance don yaki da corona

Binta Aliyu Zurmi
April 24, 2020

Gwamnatin Najeriya ta nemi bashi daga asusun bada lamuni na duniya domin yaki da annobar cutar corona da kuma aiwatar da wasu muhimman ayyukan cigaban al'umma.

https://p.dw.com/p/3bNGF
Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

Asusun bada lamuni na duniya ya tsayar da ranar 28 ga wannan watan na Afirilu don duba bukatar mahukuntan Najeriya na neman rancen kudi na gagawa na dala biliyan uku da miliyan dari hudu don fidda kasar daga halin da ta sami kanta a ciki na annobar Corona.

Kanfanin dillancin labarai na Reuters, ya ruwaito cewa tsayar da ranar tataunawar wata babar alama ce da ke nuna kasar zata sami rancen.

Ko baya ga halin ha'ulain da annobar ta corona ta jefa Najeriya a ciki dama ta shiga halin tsaka mai wuya tun bayan da farashin danyan mai ya fadi a kasuwannin duniya. 

Yanzu dai Ministan kudi ta Najeriya Zainab Ahmed na nemawa kasar rancenn kudi da jimillar su suka kai biliyan shidda da miliyan dari tara daga bankin bada lamunin da kuma wasu manyan hukumomin masu bada rance.

A cewarta za a yi amfani da kudin ne wajen biyan wasu bukatun gagawa da kuma inganta harkar lafiyar kasar.