1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta ce akwai hannun ´yan ketare a fashewar bama-bamai a New Delhi

November 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvN6

FM Indiya Manmohan Singh ya ce wadanda suka kai hare-haren bama-baman na a birnin New Delhi a karshen mako suna da alaka da wasu ´yan ketare. Ko shakka babu wadannan kalaman na Singh tamkar hannunka mai sanda yake yiwa Pakistan. Indiya dai ta sha zargin Pakistan da marawa kungiyoyin ´yan tawayen musulmi a Kashmir baya, to amma gwamnati a birnin Islamabad ta musanta wannan zargi. Jami´an Pakistan sun mayar da martani inda suka yi kira ga Indiya da ta ba da shaidar cewa akwai hannun kungiyoyin ´yan tawayen Kashmir a fashewar bama-baman da suka halaka mutane sama da 60. Hakazalika Pakistan ta yi alkawarin ba da hadin kai a binciken da ake yi. Yanzu haka dai ´yan sanda a New Delhi na yiwa mutane fiye da 24 tambayoyin a dangane da hare haren.