1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indunusiya: Za a hallaka masu safarar kwaya

Yusuf BalaJuly 26, 2016

Hukumomi a Indunusiya za su hallaka masu safarar muggan kwayoyi da aka kama ciki kuwa har da wani dan Najeriya. Kisan ya zama karo na uku karkashin gwamnatin Joko Widodo.

https://p.dw.com/p/1JWD5
Indonesien Präsident Joko Widodo
Joko Widodo ya sha alwashi na murkushe masu fasakaurin kwayoyiHoto: Getty Images/AFP/R. Rahman

Wani guggun masu laifi zai fuskanci hukuncin kisa a kasar Indunusiya a cikin wannan mako bayan da mahukunta a kasar suka bada dama ta aiwatar da hukuncinn kisan a wannan rana ta Talata. Wannan mataki dai na zuwa ne bayan sukar da shirin kisan ya sha daga masu zanga-zanga da ma kiraye-kiraye na kasa da kasa. Syed Zahid Raza mataimakin jakadan kasar Pakistan a birnin Jakarta ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cikin wadanda za a halaka a daren ranar Juma'a sun hadar da dan kasar ta Pakistan.

Baya ga dan kasar ta Pakistan akwai 'yan wasu kasashen na Najeriya da Indiya da Zimbabuwe da 'yan kasar ta Indunusiya. Jami'ai dai sun bayyana cewa babu 'yan kasashen Turai ko Ostareliya. Wannan kisa dai ya zama karo na uku karkashin gwamnatin Shugaba Joko Widodo wacce ta aiwatar da irin wannan kisa na mutane bakwai a watan Afrilun 2015 ga wasu 'yan kasashen waje da suka hadar da 'yan Ostareliya mutum biyu. Gwamantin ta Indunusiya dai na cewa ba za ta yi sassauci ba a yakin da take da masu fasakaurin miyagun kwayoyi zuwa kasar.