1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta haɗin kan taimakon raya ƙasashe masu tasowa

Mohammad Nasiru AwalFebruary 7, 2007

ƙasashen Jamus da Portugal da kuma Sloveniya sun gabatar da shirin ƙarfafa ayyukan haɗin kai a fannin taimakon raya ƙasashe masu tasowa.

https://p.dw.com/p/BvT1
Wieckzorek-Zeul da shugaban Brazil Lula da Silva
Wieckzorek-Zeul da shugaban Brazil Lula da SilvaHoto: Marcello Casal Jr.

Tun a karshen shekarun 1990 Jamus ta rage yawan kasashen da take hadin kai da su a shirin taimakon raya kasa, daga 120 zuwa 75, amma a lokaci daya ta karfafa manufofin ta a wannan fanni. A karkashin wani shiri na raba ayyuka tsakanin kasashe membobin KTT, nan gaba kadan ana iya karfafa hadin kan taimakon raya kasashe masu tasowa, inji Heidemarie Wieckzorek-Zeul ministar raya kasashe masu tasowa ta tarayyar Jamus.

“Abin da muka sa a gaba shi ne inganta yawan taimakon musamman don biyan bukatun kasashen da muke da dangantaka da su wato kasashe masu tasowa. Manufar raba ayyukan ita ce rage yawan masu ba da taimakon ga daidaikun kasashe amma a hannu daya za´a kara mayar da hankali kan wasu bangarori da kuma inganta hadin kai tsakanin masu ba da taimakon.”

Dirk Messner daraktan cibiyar nazarin manufofin raya kasashe masu tasowa ta Jamus, ya nunar a fili cewa nan gaba za´a samun cikakken hadin kai.

“Mun ba da shawarar kull wata yarjejeniya wato kamar ta tabbatar da da´a tsakanin kasashe membobin KTT. Ta haka zamu yi kokarin gane yawan masu ba da taimako ga kowace kasa da fannoni da kuma irin aikin da suke gudanarwa.”

Abin da aka sa a gaba a nan shi ne hade kan ayyukan raya kasa bayan an rage yawan kasashen Turai dake ba da taimako.

Ga ministar ba da taimakon raya kasa ta Jamus Wieckzorek-Zeul abu mafi muhimmanci shi ne Jamus ta karfafa taimakon da take bayarwa na hadin kai tsakanin ta da yankunan dabam dabam na duniya.

“Ba wani takammemen aikin da muke gudanarwa da kasashe da yawa na yankin Latunamirka, amma a hakika muna kokarin inganta hadin kai da yankuna dabam dabam a batutuwan da suka shafi yaki da kwararar hamada da kuma rikice rikice.”

Ministar ta Jamus zata kuma mayar da hankali wajen samar da tsabtataccen ruwan sha, sabbin hanyoyin na samun makamashi, kare muhalli da kuma yaki da yaduwar cutar AIDS ko Sida.

Jakadiyar Sloveniya a Jamus Dragolyuba Bencina ta jawo hankali cewa kasarta zata kara mayar da hankali wajen taimakawa kananan yara da mata a yankunan da ake fama da yake yake.

Ita kuwa Portugal wadda ke da kwarewa a aikin raya kasa yanzu haka ita da NL da Luxemburg na tafiyar da ayyukan raya kasa a Cape Verde da wasu kasashe masu tasowa.